Rikicin Kungiyar Ohanaze Ndgibo yayi kamari a dalilin zaben 2019

Rikicin Kungiyar Ohanaze Ndgibo yayi kamari a dalilin zaben 2019

Mun ji cewa Babban Sakataren kungiyar nan na mutanen Ibo watau Ohanaeze Ndigbo, mai suna Uche Okwukwu, ya bayyana cewa ba su tare da mubaya’ar da aka ce kungiyar tayi wa Atiku Abubakar na PDP.

Rikicin Kungiyar Ohanaze Ndgibo yayi kamari a dalilin zaben 2019

An samu sabani tsakanin manyan Kungiyar Ohanaze Ndgibo
Source: Depositphotos

Kamar yadda mu ka ji, Uche Okwukwu, ya tabbatarwa ‘yan jaridar Daily Sun cewa an ci albasa da bakin su wajen tsaida Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa a matsayin ‘dan takakar da Ohanaeze Ndigbo ta amince da shi a zaben bana.

Cif Okwukwu yace a matsayin sa na Sakataren kungiyar, babu inda ya sa hannu cewa za su marawa Atiku baya a zaben da za ayi a cikin watan nan. Wannan ya sa Okwukwu ya ke ganin cewa mubaya’ar da aka yi wa Atiku ba za ta sabu ba.

KU KARANTA: Buhari ya so ace Inyamuri ya zama Shugaban Majalisa a 2015 – Uba

Sakataren kungiyar ta Ohanaeze yace manyan su ba su wajen taron da shugaban Ohanaeze ya bayyana Atiku a matsayin ‘dan takarar su a zaben bana. Yace shugaban kungiyar yaci amanar Inyamurai da wannan mataki da ya dauka shi kadai.

Sakataren Kungiyar na Ohanaeze ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Buhari ta APC tana kokarin sauya-fasalin Najeriya inda yace za a ba yankin kasar Inyamurai karin jiha guda nan gaba domin a samu daidaito a fadin Najeriya.

Kwanaki kun ji cewa kamar dai gwamnan Anambra, Sakataren kungiyar ta Ohanaeze Ndigbo yayi kira ga jama’a suyi watsi da John Nwodo su marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC mai mulki baya a zaben wannan karo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel