Dalilin da yasa tsofin janar na soji ba sa tare da Buhari - Oshiomhole

Dalilin da yasa tsofin janar na soji ba sa tare da Buhari - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya ce manyan tsofin janar na soji da ke kasar nan na kulle-kullen kawo karshen gwamnatin shugaba Buhari ta kowacce hanya.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin gabatar da tutar takarar ga gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, dan takarar gwamna a jam'iyyar APC, a filin taro na Malam Aminu Kano da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Ya bayyana cewar tspfin janar din sojin na son ganin bayan gwamnatin shugaba Buhari ne saboda irin aiyukan da Buhari ke yi ga jama'ar Najeriya ya saba wa bukatun su.

Oshiomhole ya kara da cewar sha'awar shugaba Buhari na son kyautata wa talaka ne babban dalilin da yasa tun a farko tsofin janar na sojin ke murde shi zabe tun a baya.

Dalilin da yasa tsofin janar na soji ba sa tare da Buhari - Oshiomhole

Buhari da Oshiomhole
Source: Depositphotos

Shugaban jam'iyyar na APC ya bayyana cewar Allah ne ya turo Buhari domin ya tsamo Najeriya daga turbar rushewa da shugabanni marasa kishi su ka dora ta a baya.

Kazalika, ya bukaci jama'a da su kada kuri'un su ga shugaba Buhari da 'yan takarar jam'iyyar APC tare yin kira gare su da kar su bari jam'iyyar adawa ta yaudare su da alkawuran bogi da romon baka.

DUBA WANNAN: Siyasar Kano: Dalilin da ya sa ban halarci mahawarar 'yan takara ba - Ganduje

Dubun dubatar masoya da magoya bayan shugaba Buhari da jam'iyyar APC ne su ka halarci taron yakin neman zaben da aka gudanar a Aminu Kano Square da ke garin Dutse, babbab birnin Jigawa.

Shugaba Buhari da tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC sun dira a garin Dutse bayan kammala taron yakin neman zabe a jihar Gombe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel