Badakalar makamai: Fayose zai gurfana gaban kotu a ci gaban shari'arsa da EFCC

Badakalar makamai: Fayose zai gurfana gaban kotu a ci gaban shari'arsa da EFCC

- A ranar Litinin, 4 ga watan Fabreru, kotu za ta ci gaba da sauraron karar da hukumar EFCC ta shigar akan tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mr Peter Ayodele Fayose

- EFCC na zargin Fayose da karbar akalla N7.2bn daga tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa Jonathan ta fuskar tsaro, Sambo Dasuki

- Tuni dai Obanikoro, wanda EFCC ta gabatarwa kotu a matsayin shaida, ya tabbatar da cewa ya ba Fayose tsabar kudi har $5m da ya ciro daga asusun tsaro na kasa

A ranar Litinin, 4 ga watan Fabreru, kotu za ta ci gaba da sauraron karar da hukumar da ke yaki da masu yiwa dukiyar gwamnati zagon kasa (EFCC) ta shigar akan tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mr Peter Ayodele Fayose, kan zarginsa da handame N7.2bn.

Shari'ar wacce ke gaban mai shari'a Mojisola Olatoregun na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Legas inda tsohon ministan cikin gida kan harkokin tsaro, Sanata Musiliu Obanikore ke ci gaba da amayar da gaskiya kan wannan zargi da ake yiwa Fayose.

Obanikoro, wanda EFCC ta gabatarwa kotu a matsayin shaida, ta hannun lauyan hukumar, Mr Rotimi Jacobs SAN, a zaman kotun na karshe da ya gabata, ya bada shaidar cewa ya ba Fayose tsabar kudi har $5m da ya ciro daga asusun tsaro na kasa bisa umurnin mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fuskar tsaro, Sambo Dasuki.

KARANTA WANNAN: Hatsarin jirgi: Buhari ya jinjinawa jajurcewar Osinbajo na ci gaba da yakin zabe

Badakalar makamai: Fayose zai gurfana gaban kotu a ci gaban shari'arsa da EFCC

Badakalar makamai: Fayose zai gurfana gaban kotu a ci gaban shari'arsa da EFCC
Source: Facebook

Har yanzu dai shima Dasuki na ci gaba da fuskantar tuhuma kan badakalar $2.1bn da aka ware su domin sayawa sojoji makaman da za su yaki 'yan ta'addan Boko Haram a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015.

Fayose ya bukaci a dage sauraron sha'ri'ar, ta hannun lauyoyinsa, Kanu Agabi SAN da Olalekan Ojo SAN, domin ba su damar yin kyakkyawan nazari akan Obanikoro.

Mai shari'a Olatoregun, wanda ya sanya ranakun 4 zuwa 5 ga watan Fabreru a matsayin ranakun ci gaba da sauraron shari'ar ya ce wannan shine karo na karshe da za a dage shari'ar a madadin wadanda ake karar, har zuwa lokacin da shari'ar za ta zo karshe.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel