Ina jajantawa Osinbajo kan tsautsayi na hatsarin jirgi - Kwankwaso

Ina jajantawa Osinbajo kan tsautsayi na hatsarin jirgi - Kwankwaso

Mun samu cewa, tsohon gwamna kuma wakilin shiyyar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya yi furuci dangane da samu labarin sa na kifewar jirgin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a jiya Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa, a jiya Asabar jirgi mai saukar angulu dauke da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da kuma tawagar sa, ya kife yayin ziyarar sa ta zuwa garin Kabba na jihar Kogi domin gudanar da taron yakin neman zabe.

Ina jajantawa Osinbajo kan tsautsayi na hatsarin jirgi - Kwankwaso

Ina jajantawa Osinbajo kan tsautsayi na hatsarin jirgi - Kwankwaso
Source: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Kwankwaso, cikin dattako da kuma ajiye adawa irin ta akidar siyasa, ya jajantawa mataimakin shugaban kasa sakamakon wannan tsautsayi da ya sake aukuwa akan sa bayan makamancin wanda ya auku akan sa cikin garin Abuja a shekarar 2017 da ta gabata.

Sanata Kwankwaso cikin wani sako da ya wassafa a shafin sa na zauren sada zumunta, ya yi babbar godiya ga Mahallacin Sammai da Kassai da ya tsare lafiyar mataimakin shugaban kasa yayin da jirgin sa ya kife kuma dukkanin wandan ke cikin sa suka tsira lafiya ba tare da ko kwarzane ba.

KARANTA KUMA: Sai na aske gashi na idan Buhari yayi nasara a zaben 2019 - Bello Muhammad

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan lamari na ibtila'i bai haramtawa mataimakin shugaban kasar gudanar da taron sa na yakin neman zabe a jihar Kogi cikin karsashi da koshin lafiya kamar yadda kudirta.

Kazalika shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, yayin mika sakon su na jaje ga Osinbajo, sun kuma yabawa jarumtar sa tare da bayyana farin cikin su dangane da yadda ya kwashe lafiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel