Hatsarin jirgi: Buhari ya jinjinawa jajurcewar Osinbajo na ci gaba da yakin zabe

Hatsarin jirgi: Buhari ya jinjinawa jajurcewar Osinbajo na ci gaba da yakin zabe

- Shugaba Buhari ya jinjinawa kokarin mataimakinsa, Yemi Osinbajo, na ci gaba da yakin zabensa a jihar Kogi duk da cewar jirgin da yake dauke da su ya yi hatsari

- Jawabin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasa Buhari ta fuskar watsa labarai, Garba Shehu

- Daga karshe shugaban kasar ya roki Allah ya ci gaba da kare mataimakin nasa da dukkanin wadanda hatsarin ya rutsa da su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa kokarin mataimakinsa, Yemi Osinbajo, na ci gaba da yakin zabensa a jihar Kogi duk da cewar jirgin da yake dauke da su ya yi hatsari a garin Kabba da ke jihar a ranar Asabar, 2 ga watan Fabreru, 2019.

Da ya ke tsokaci kan hatsarin da ya faru jiya a cikin wayar tarho da ya kira mataimakin nasa, shugaban kasar ya fara yiwa Allah godiya akan yadda ya tsare rayukan mutanen da ke cikin jirgin, tare da nuna tsantsar jinjinawa ga mataimakin nasa na nuna juriya da nutsuwa da har ya samu karfin guiwar ci gaba da yakin zaben da ya kaisa jihar.

Jawabin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasa Buhari ta fuskar watsa labarai, Garba Shehu, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook a safiyar Lahadi, 3 ga watan Fabreru, 2019.

KARANTA WANNAN: Hadimin Buhari: Yadda muka rayu bayan faduwar jirgi tare da Osinbajo

Hatsarin jirgi: Buhari ya jinjinawa jajurcewar Osinbajo na ci gaba da yakin zabe

Hatsarin jirgi: Buhari ya jinjinawa jajurcewar Osinbajo na ci gaba da yakin zabe
Source: UGC

Shugaban kasa Buhari ya ce: "Hakika sai mutum mai matukar karfin imani da karfin zuciya irin ta mazaje ba ragwaye ba, a ce kayi hatsarin jirgin sama amma ka ci gaba da ayyukanka ba tare da hatsarin ya taba lafiyar tunaninka ba. Ina matukar alfahari da irin namijin kokarin da ka nuna da kuma kokarinka na yiwa kasarka hidima a cikin kowanne hali ka tsinci kanka."

"Ci gaba da harkokin da ya kaika garin, duk da cewa hatsarin ya rutsa da kai, babbar alama ce da ke nuna cewa ci gaban kasar ne a zuciyarka da kuma kwarin guiwar da kake da shi."

Daga karshe shugaban kasar ya roki Allah ya ci gaba da kare mataimakin nasa da dukkanin wadanda hatsarin ya rutsa da su, da rokon Allah ya albarkaci kasar Nigeria da wadatuwar arziki da kuma dorewar rayuwa mai albarka domin kai kasar tudun mun tsira.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel