Da dumin sa: Wasu 'yan bindiga sun budewa direbobi da matafiya wuta a wata jihar Arewa

Da dumin sa: Wasu 'yan bindiga sun budewa direbobi da matafiya wuta a wata jihar Arewa

Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga dadi ne sun budewa wuta direbobi da matafiya wuta a kan titin da ya ratsa karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara zuwa Gurbin-Baure na karamar hukumar Jibiya, jihar Katsina.

Harin 'yan bindigan dai kamar yadda muka samu ya yi sanadiyyar mutuwar akalla wani direba guda da kuma sace mutanan da kawo yanzu ba a san adadin su ba.

Da dumin sa: Wasu 'yan bindiga sun budewa direbobi da matafiya wuta a wata jihar Arewa

Da dumin sa: Wasu 'yan bindiga sun budewa direbobi da matafiya wuta a wata jihar Arewa
Source: Twitter

KU KARANTA: Hanyoyi 2 da Atiku ya zarta Buhari - Buba Galadima

Mazauna yankin dai da suka zanta da majiyar mu sun shaida mata cewa da misalin karfe uku da minti biyar na rana ne 'yan bindigar suka tare hanya tare da bude wuta a kan masu wuce wa da kuma kona mota guda.

Legit.ng Hausa ta samu cewa wadanda lamarin ya auku akan idon su sun bayyana cewa kafin jami'an tsaro su isa yankin da abin ya faru 'yan bindigar sun tsere. sun shiga daji wanda hakan ne ma ya haifar da fargaba tsakanin mazauna yankin da ke zaman dar-dar a yanzu.

An dai kashe daruruwan mutane a Zamfara a tsawon shekara shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar.

Hare-haren da barayin shanu da masu satar mutane don kudin fansa ke yi a Zamfara na karuwa, duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen ayyukansu.

Gwamnatin jihar ta sha cewa tana daukar mataki domin shawo kan matsalar, ko da yake ana zarginta da hannu a batun amma ta musanta zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel