Fusatattun matasa sun kai hari ofishin INEC, sun kona katin zabe ma su yawa

Fusatattun matasa sun kai hari ofishin INEC, sun kona katin zabe ma su yawa

Katinan zabe na dun-dun-dun da ma su shi basu karba ba sun sha wuta bayan wasu fusatattun matasa da ba a san ko su waye ba sun kai hari ofishin hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) dake karamar hukumar Isialangwa ta kudu a karamar jihar Abia.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage sati biyu a gudanar da zaben shugaban kasa a jerin zabukan da za a gudaar a shekarar nan.

Joseph Iloh, kwamishinana hukumar zabe a jihar Abia, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau, Lahadi.

"An shawo kan wutar da kyar, amma dakin da ake ajiye katinan zabe ya kone kurmus, katinan zabe na dun-dun-dun da ba a karba ba duk sun kone," kamar yadda Ndedu Ekeke ya bayyana a shafinsa na Tuwita.

Fusatattun matasa sun kai hari ofishin INEC, sun kona katin zabe ma su yawa

Fusatattun matasa sun kai hari ofishin INEC, sun kona katin zabe ma su yawa
Source: Twitter

Ekeke ya bayyana cewar fusatattun matasan sun kai farmaki ofishin zaben ne domin kawai su kone katinan zaben jama'a da ke hannun hukumar INEC.

Ya kara da cewa a kalla katinan zabe 1,500 ne su ka kone tare da rijistar da ke dauke da sunayen ma su kada kuri'a.

DUBA WANNAN: Kamfen din Buhari: Mutane 2 sun suma a jihar Jigawa

Sannan ya kara da cewa, duk da haka, hukumar INEC na da dukkan sunayen ma su kada kuri'a a babbar rijistar ma su zabe ta kasa da ke hedikwatar ta a Abuja.

Rundunar 'yan sanda a jihar Abia ta bayyana cewar ta na gudnar da bincike a kan lamarin tare da bayyana cewar za ta tabbatar wadanda su ka aikata wannan laifi sun shiga hannu domin a gurfanar da su a gaban shari'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel