Hatsarin jirgi ya rutsa da ni amma na rayu - Osinbajo ya godewa Allah a majami'a

Hatsarin jirgi ya rutsa da ni amma na rayu - Osinbajo ya godewa Allah a majami'a

Yanzu Legit.ng Hausa ta samu rahoto daga shafin jaridar Daily Trust, inda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yanzu yake halartar wani taron addu'a na musamman a majami'ar Reedemed Christian Church of God (RCCG), da ke birnin Grace, jihar Lokoja.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa jirgi mai saukar angulu, dauke da mataimakin shugaban kasa da wasu mutane akalla 13, ya yi hatsari da su a lokacin da ya zo sauka garin Kabba, jihar Kogi, sai dai babu wanda ya ji rauni daga mahaya jirgin.

Ana haska wannan taron addu'ar ta musamman a manyan gidajen talabijin, wanda ke gudana karkashin babban shugaban majami'ar RCCG, Fasto Enoch Adeboye, na shelkwatar majami'ar da ke Legas.

KARANTA WANNAN: Jirgi dauke da Yemi Osinbajo ya yi hatsari - Ga bidiyon yadda jirgin ya fadi

Hatsarin jirgi ya rutsa da ni amma na rayu - Osinbajo ya godewa Allah a majami'a

Hatsarin jirgi ya rutsa da ni amma na rayu - Osinbajo ya godewa Allah a majami'a
Source: Twitter

Adeboye, wanda ya jagoranci taron addu'ar da bauta ta musamman, ya godewa Allah da ya ceci rayukan mataimakin shugaban da sauran tawagarsa, ba tare da ya barsu sun mutu a cikin hatsarin jirgin ba.

Kalli bidiyon yadda jirgin da ke dauke da Yemi Osinbajo ya yi hatsari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel