Bayan rikotowar jirgi, Osinbajo ya gudanar da yakin neman zabe a jihar Kogi

Bayan rikotowar jirgi, Osinbajo ya gudanar da yakin neman zabe a jihar Kogi

A jiya Asabar 2 ga watan Fabrairu, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci birnin Lokoja na jihar Kogi domin taron yakin neman zabe da girgiza magoya baya yayin da babban zaben kasa ya ke ci gaba da karatowa.

Bayan rikotowar jirgi, Osinbajo ya gudanar da yakin neman zabe a jihar Kogi

Bayan rikotowar jirgi, Osinbajo ya gudanar da yakin neman zabe a jihar Kogi
Source: Twitter

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, gabanin wannan taro, tsautsayi ya afka kan mataimakin shugaban kasar yayin da jirgi mai saukar angulu da ya yo jigilar sa ya kife a garin Kabba. Sai dai ya yi sa'ar gaske ba bu kwarzane da ya samu.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, shine ya bayar da shaidar hakan da cewar jirgin na dauke ne da Mataimakin shugaban kasa, Sanata Babafemi Ojudu da kuma likitan uwar gidan mataimakin shugaban kasar.

KARANTA KUMA: Kwankwaso ya wakilci Atiku yayin bikin kaddamar da littafi a garin Abuja

Majiyar mu ta jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari bai kawo wata tangarda ta gudanar da yakin neman zabe da mataimakin shugaban kasar ya kudirci aiwatar wa a garin Kabba na jihar Kogi.

Ko shakka ba bu jiga-jigan kasar nan sun janjantawa mataimakin shugaban kasar dangane da wannan tsautsayi da ya auku tare da bayyana farin cikin su sakamakon yadda ya tsira tare da tawagar sa ba tare da ko kwarzane guda ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel