Hadimin Buhari: Yadda muka rayu bayan faduwar jirgi tare da Osinbajo

Hadimin Buhari: Yadda muka rayu bayan faduwar jirgi tare da Osinbajo

Babafemi Ojudu, wani hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar harkokin siyasa, a ranar Lahadi ya godewa jami'an kai agajin gaggawa da suka kai masu daukin ceto a lokacin da jirgi mai saukar angulu da suke ciki ya yi hatsari tare da faduwa a ranar Asabar.

Mr Ojudu yana daya daga cikin tawagar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinba a lokacin da lamarin ya afku, a lokacin da jirgin ke kokarin sauka a garin Kabba, jihar Kogi.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa jirgin ya fadi ne da misalin karfe 3:00 na rana, inda Messr Osinbajo da Ojudu suka tsira da rayukansu ba tare da ko kwarzane ba, tare da wasu mutane 10 da ke cikin jirgin. Ministan cikin gida kan harkokin kwadago da kere kere, Stephen Ocheni, na daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su.

KARANTA WANNAN: Yan ta'adda sun tayar da tarzoma a yakin zaben APC, mutum 1 ya mutu, 2 sun jikkata

Hadimin Buhari: Yadda muka rayu bayan faduwar jirgi tare da Osinbajo

Hadimin Buhari: Yadda muka rayu bayan faduwar jirgi tare da Osinbajo
Source: UGC

Kamfanin Coverton, kamfanin jiragen sama da ke kula da jirgi mai saukar angulu mai suna "Ausgusta A139", ya ta'allaka wannan hatsarin da gurbacewar yanayi a sararin samaniya. Sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan sanadin faduwar jirgin.

Hadimin shugaban kasar ya yi jawabi jim kadan bayan faruwar hatsarin, yana mai cewa gaba daya wadanda ke cikin jirgin suna cikimn koshin lafiya, inda har suka ci gaba da harkokinsu na yakin zabe kamar yadda aka tsara.

'Yan Nigeria daga mabanbanta jam'iyyun siyasa da addinai sun taya mataimakin shugaban kasar, Mr Osinbajo da sauran wadanda suke cikin jirgin murnar tsira da rayukansu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel