Ana-wata-ga-wata: Tsarin mafi karancin albashi na Naira dubu 30 ya gamu da babban cikas

Ana-wata-ga-wata: Tsarin mafi karancin albashi na Naira dubu 30 ya gamu da babban cikas

Da alama dai matsayar da kungiyar kwadago ta Najeriya ke muradin cimmawa da mahukuntan kasar Najeriya musamman a game da tsarin mafi karancin albashi na Naira dubu 30 na shirin gamuwa da wani cikas, kamar dai yadda majiyar mu ta tabbatar.

A satin da ya gabata ne dai ranar majalisar wakillan tarayyar Najeriya ta zartar da kudurin mafi karancin albashin ma'aikatan kasar na Naira dubu 30 sabanin Naira dubu 27 din da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura masu a matssayin kuduri.

Ana-wata-ga-wata: Tsarin mafi karancin albashi na Naira dubu 30 ya gamu da babban cikas

Ana-wata-ga-wata: Tsarin mafi karancin albashi na Naira dubu 30 ya gamu da babban cikas
Source: UGC

KU KARANTA: Wani fasto da mabiyan sa sun shiga musulunci a Ilori

Sai dai mai karatu zai iya tuna cewa suma mambobin kwamiti na musamman da gwamnatin tarayya ta kafa mai bangarori uku a cikin rahoton su da suka gabatarwa shugaban kasa, sun bayar da shawarar Naira dubu 30 ne a matsayin mafi karancin albashi.

Yanzu dai kamar yadda muka samu shugaban kasa na fuskantar matsin lamba ne daga wasu gwamnonin jahohin kasar nan wadanda ke ikirarin cewa ba za su iya biyan hakan ba wajen ganin bai sanyawa dokar hannu ba.

Sai kuma shugabannin kwadago tuni suka sha alwashin sa kafar wando daya da dukkan wanda zai kawowa batun karin albashin cikas ko mai matsayin sa kamar dai yadda shugaban kwadagon, Mista Ayuba Wabba ya sha alwashi hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel