Yan ta'adda sun tayar da tarzoma a yakin zaben APC, mutum 1 ya mutu, 2 sun jikkata

Yan ta'adda sun tayar da tarzoma a yakin zaben APC, mutum 1 ya mutu, 2 sun jikkata

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'adda sun farwa mambobin jam'iyyar APC a yayin da suke gudanar da gangamin yakin zabensu a garin Sagbama da ke jihar Bayelsa

- A sanadin kai harin, mutane biyu sun jikkada, ya yin da mutum daya ya mutu bayan samun munanan raunuka

- DSP Asinim Butswat, ya ce rundunar 'yan sanda a jihar ta samu nasarar cafke daya daga cikin 'yan ta'addan da suka kai wannan hari

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'adda sun farwa mambobin jam'iyyar APC a yayin da suke gudanar da gangamin yakin zabensu a garin Sagbama da ke jihar Bayelsa, harin dai ya jawo asarar ran mutum daya da jikkata mutane biyu.

Wani mazaunin garin Sagbama wanda harin ya faru akan idanunsa ya ce akalla 'yan ta'addan sun kai 15, inda suka yi amfani da muggan makamai wajen tarwatsa jama'ar da ke a filin yakin zaben.

Kawo agajin gaggawa da rundunar 'yan sanda ta yi a wajen ya hana lamarin kara munana, a cewar mazaunin garin.

KARANTA WANNAN: Dalibai ku kwantar da hankalinku: Yau ASUU za ta janye yajin aiki - Adamu Adamu

Yan ta'adda sun tayar da tarzoma a yakin zaben APC, mutum 1 ya mutu, 2 sun jikkata

Yan ta'adda sun tayar da tarzoma a yakin zaben APC, mutum 1 ya mutu, 2 sun jikkata
Source: Depositphotos

Wata majiya ta bayyana cewa, "Gwamnan jihar Bayelsa wanda shi ne jagoran jam'iyyar Adawa ta PDP ya fito ne daga garin Sagbama, kuma ana ganin garin a matsayin mallakin PDP, kusan rikicin dai ya tashi ne saboda adawa ta siyasa."

DSP Asinim Butswat, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya ce rundunar ta samu nasarar cafke daya daga cikin 'yan ta'addan da suka kai wannan hari.

"A yayin farmakin da 'yan ta'addan suka kai, wani mazaunin garin Tungbabiri, mai suna Braye Embikorobiri ya samu mummunan rauni, inda daga baya ya mutu. Wasu kuma mutane biyu da suka jikkata suna kwance asibiti yanzu ana masu jinya," a cewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel