Dalibai ku kwantar da hankalinku: Yau ASUU za ta janye yajin aiki - Adamu Adamu

Dalibai ku kwantar da hankalinku: Yau ASUU za ta janye yajin aiki - Adamu Adamu

- A ranar Asabar, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa a yau Lahadi, 3 ga watan Fabreru zata tabbata ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i suke kan yi

- A yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da yin zaman sulhu, har zuwa yanzu, babu wani zama da ya haifar da d'a mai ido

- Sai dai Ministan ilimi, Adamu Adamu, ya ce tuni dai gwamnatin tarayya ta cimma matsaya da ASUU, kuma ana sa ran kungiyar za ta janye yajin aikin nata a yau Lahadi

A ranar Asabar, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa a yau Lahadi, 3 ga watan Fabreru zata tabbata ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i suke kan yi, domin baiwa dalibai damar komawa makarantunsu.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2018, bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan bukatun da ta gabatar.

Wannan yajin aikin ya kawo tsaikon koyo da koyarwa a jami'o'i da ke fadin kasar.

KARANTA WANNAN: Yanzunnan: Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin zabensa a jihar Abia cikin salo

Kowa ya kwantar da hankalinsa: Yau ASUU za ta janye yajin aiki - Adamu Adamu

Kowa ya kwantar da hankalinsa: Yau ASUU za ta janye yajin aiki - Adamu Adamu
Source: Facebook

A yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da yin zaman sulhu, har zuwa yanzu, babu wani zama da ya haifar da d'a mai ido.

Sai dai Ministan ilimi, Adamu Adamu, a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce tuni dai gwamnatin tarayya ta cimma matsaya da ASUU, kuma ana sa ran kungiyar za ta janye yajin aikin nata a yau Lahadi.

Ya ce: "Yau (Asabar) za su janye yajin aikin ko gobe (Lahadi), kuma muna da tabbacin cewa, ba zamu shiga mako na gaba cikin yajin aikin ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel