Andy Uba yana hangen mukamin Shugaban Majalisa Dattawa idan ya zarce

Andy Uba yana hangen mukamin Shugaban Majalisa Dattawa idan ya zarce

Mun ji labari cewa Sanata Andy Uba wanda yake wakiltar Kudancin jihar Anambra ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa idan ya zarce a kan kujerar sa.

Andy Uba yana hangen mukamin Shugaban Majalisa Dattawa idan ya zarce

Sanata Uba ya fara harin kujerar Bukola Saraki bayan zaben bana
Source: UGC

Any Uba wanda yanzu haka Sanatan jam’iyyar APC mai mulki ne yana ganin cewa zai iya samun kujerar shugaban majalisar dattawan Najeriya bayan zaben 2019. Sanatan yace hakan zai yiwu ne idan har yayi nasara a zaben da za ayi.

Sanata Uba yayi wannan jawabi ne a cikin Garin Orumba a jihar Anambra lokacin da yake yawon kamfe. Sanatan ya fadawa mutanen sa su sake zaben a bana sa domin mutanen kudu maso Gabas su fito da shugaban majalisa a Najeriya.

KU KARANTA: Tsoron a tsige sa ya Saraki ya fasa bude Majalisa a makon jiya

‘Dan majalisar yake cewa shugaba Buhari yayi kokarin ganin mutumin kasar Ibo ne ya zama shugaban majalisar dattawa bayan zaben 2015. Uba yace hakan bai yiwu bane bayan an gaza samun Sanatan APC daga can kudancin kasar.

Sanatan na Anambra yana ganin cewa muddin ya sake komawa majalisa a wannan karo, babu mamaki ya karbe kujerar Bukola Saraki. Uba ya kuma nemi jama’a su mara masa da shi da Buhari baya a APC a zaben da za ayi a tsakiyar watan nan.

Andy Uba wanda ya dade a Majalisa ya na ganin cewa zaben Sanatan sa ya zarce na gwamnan jiha amfani domin kuwa Anambra za ta iya tashi da kujerar shugaban majalisar dattawa wanda yake da matukar muhimmanci a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel