Zaben 2019: Jam’iyyar APC ce za ta samu gagarumar nasara – Kayode Ajulo

Zaben 2019: Jam’iyyar APC ce za ta samu gagarumar nasara – Kayode Ajulo

- Dr. Kayode Ajuola yace Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019

- Dr. Ajulo shi ne Sakataren Kungiyar nan ta Forward With Buhari

- Ajulo yace ya bar Jam’iyyar Labor domin yayi wa Buhari kamfen

Zaben 2019: Jam’iyyar APC ce za ta samu gagarumar nasara – Kayode Ajulo

Tsohon Sakataren Jam’iyyar LP ya koma yi wa Buhari kamfe
Source: Facebook

Mun ji cewa fitaccen ‘dan gwagwarmayar nan watau Kayode Ajulo yayi magana game da zaben 2019 inda yace babu wata tababa cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai lashe zaben da za ayi nan da wasu ‘yan kwanaki.

Dr. Kayode Ajulo wanda ya bar kujerar sa na babban Sakataren jam’iyyar Labour Party na Najeriya domin ganin ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe, yace APC za tayi nasara a jihohi har 30 na Najeriya.

KU KARANTA: Inda Atiku ya sha ban-bam da Shugaba Buhari - Buba Galadima

Kayode Ajulo yana ganin cewa Atiku Abubakar wanda shi ne ke rike da tutar jam’iyyar hamayya, ba zai kai labari ko a jihar sa ta Adamawa ba. Shugban kungiyar siyasar nan ta Forward with Buhari, Ajuolo ya fadi haka ne kwanan nan.

Dr. Ajulo yake cewa APC tayi karfi a kaf jihohin Najeriya 36, da kuma kananan hukumomi 774 da ake da su, da duk wata tashar zabe don haka yake ganin cewa shugaba Buhari zai samu makudan kuri’u a zaben da za ayi kwanan nan.

Ko da dai har yanzu Kayode Ajulo bai yanki katin zama ‘dan jam’iyyar APC ba, ya bayyana cewa za su yi iyakar kokarin su wajen ganin shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zaben 2019 domin ganin ya zarce a kan karagar mulkin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel