Gudun a tsige Saraki ya sa Majalisa ta ja baya ta dage zama a makon nan

Gudun a tsige Saraki ya sa Majalisa ta ja baya ta dage zama a makon nan

Kwanaki ne shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya nemi ‘yan majalisa su dawo bakin-aiki bayan samun labarin cewa shugaban kasa Buhari ya dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya daga mukamin sa.

Gudun a tsige Saraki ya sa Majalisa ta ja baya ta dage zama a makon nan

'Yan Majalisan APC sun shirya taba Saraki da zarar ya kira zama
Source: Facebook

Daga baya shugaban majalisar kasar ya janye wannan shiri inda ya dage zaman Sanatocin har sai zuwa bayan zaben shugaban kasa a cikin watan nan. Jaridar The Sun tace Bukola Saraki ya ji tsoron a tsige sa ne don haka ya dakatar da shirin na sa.

Majiyar mu ta bayyana mana cewa Saraki yayi kuskure da yayi gigin neman ya kira ‘yan majalisa a zauna a makon da ya gabata a saboda dakatar da Mai shari’a Walter Onnoghen da aka yi a matsayin shugaban Alkalan Najeriya a watan jiya.

Hadiman Bukola Saraki sun samu labari cewa da zarar an dawo aiki a majalisa, za a nemi a sauke sa daga kan kujerar sa. Wannan ya sa Saraki yayi wuf ya fitar da jawabi cewa majalisar dattawa ta kai karar gwamnatin tarayya zuwa gaban kotun koli.

KU KARANTA: An gano karyar aikin ruwan da Bukola Saraki yayi a lokacin yana gwamna

Majalisar dattawan tana neman babban kotu koli na kasar tayi mata fashin baki game da nada sabon Alkalin Alkalai da aka yin a rikon kwarya ba tare da bin doka ba. Hadimin shugaban majalisar, Yusuf Olaniyonu ne ya fitar da jawabin.

A ka’ida ya kamata ace Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya sa hannu a wannan bayani a madadin sauran Sanatocin kasar tun da shi ne ke magana da yawun bakin majalisar. Sai dai da alamu Sanata Aliyu Sabi yana cikin masu yaki da Saraki a majalisar.

Bukola Saraki ya sheka kotu ne a madadin sauran ‘yan majalisar kasar ba tare da ya tuntubi sauran Sanatocin APC ba. Fadar shugaban kasa ita kuma tayi maza-maza ta kira taro da Sanatocin APC domin ganin an takawa Bukola Saraki burki a majalisar.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za tayi maganin Bukola Saraki a inda ya ke takama

Saraki wanda a lokacin da duk wannan ya faru ba ya Abuja, ya fahimci hadarin kiran taron Sanatocin zuwa ga wani zaman gaggawa don haka ya sanar da cewa sai bayan zabe majalisa za ta sake zama domin ya tsira da kujerar sa zuwa wannan lokaci.

Yanzu dai APC ce ke da rinjaye a majalisar dattawa duk da cewa shugabannin majalisar; Bukola Saraki da Ike Ekweremadu sun fito ne daga jam’iyyar adawa. Sanatocin APC din na iya neman sauke Saraki muddin ya nemi ya kawowa shugaban kasa cikas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel