Malaman zabe kurum su ke da hurumin sanar da sakamako inji INEC

Malaman zabe kurum su ke da hurumin sanar da sakamako inji INEC

- Hukumar zabe na INEC tayi gargadi game da fitar da sakamakon karya

- INEC tace ana iya garkame masu yada sakamakon zaben bogi a kurkuku

- Hukumar mai zaman kan-ta ta gargadi ‘yan jarida su bi doka a zaben bana

Malaman zabe kurum su ke da hurumin sanar da sakamako inji INEC

INEC ta gargadi Jama’a game da fitar da sakamakon zabe
Source: UGC

Hukumar zabe na INEC mai zaman kan-ta a Najeriya ta ja kunnen jama’a da su gujewa yada sakamakon zaben da bai inganta ba a zaben bana da za ayi. Yanzu dai saura kusan makonni 2 ne kacal a fara babban zabe a Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari, wani babban kwamishinan hukumar INEC, Festus Okoye, ya gargadi mutanen gari game da sanar da sakamakon zabe. Hukumar tace sabawa hakan na iya jawowa mutum daurin shekaru a gidan yari.

KU KARANTA: INEC za ta fuskanci fushin yan Najeriya idan ta murde zabe - PDP

Kwamishinan na INEC yace aikin Baturen zabe ne sanar da sakamako ba wani ‘dan jarida ko wani mutum ba, a dalilin haka ne aka ja hankalin jama'a cewa ba su da hurumin sanarwa ko kuma yadawa Duniya sakamakon zaben kasar.

Okoye yake cewa irin wannan karam-bani ya sabawa sashe na 123(4) na dokar zabe na INEC. Idan aka samu mutum da laifin hakan, zai fuskanci hukuncin dauri a gidan maza na tsawon akalla shekaru 3 inji hukumar mai zaman kan-ta.

Bayan nan kuma hukumar mai gudanar da zabe, ta yi wa ‘yan jarida da sauran masu ruwa-da-tsaki a sha’anin zabe karin haske game da abubuwan da ba su halatta ayi wajen zabe ba. Okoye yace akwai bukatar a ilmantar da mutane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel