Jam'iyyar AA ta Rochas a Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan

Jam'iyyar AA ta Rochas a Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan

- Jam'iyar Action Alliance( AA) ta fara gudanar da kamfe dinta a jihar Imo

- Yan takarar sunce banda Buhari jam'iyar AA kadai zasu kadawa kuri'a a jihar

- Jam'iyar ta AA tace Muhammad Buhari yaci zabe ya gama

Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan

Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan
Source: Facebook

Jam'iyar nan ta Action Alliance ta fara gudanar da kamfe dinta a kananam hukumomin jihar Imo a ranar Litinin dan yada manufar shugaban kasa Muhammad Buhari.

A yayin gudanar da wannan gangami a Okwe dake karamar hukumar Onuimo jam'iyar tace "Buhari yaci zabe ya gama".

Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan

Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan
Source: Facebook

Dan takarar gwamna a jam'iyar ta AA Uche Nwosu da dan takarar sanata Ndubuisi Emenike da dantakarar majalisar jihar ta Imo Simeon Iwenzu sun bayyana cewa Buhari yanada goyan baya a jihar.

Yan takarar sun ara da cewa banda Buhari jihar jam'iyar AA kadai zasu zaba.

Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan

Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan
Source: Facebook

Nwosu ya bayyana cewa "yana da tabbacin shugaban kasa Muhammad Buhari zaici zaben da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu,ku zabi Muhammad Buhari a jam'iyar APC sannan ku zabi ragowar yan takarar dake jam'iyar AA".

"Zanyi aiki tukuru tamkar matashi sannan zan bada gudummawa sosai a bangaren noma zan kuma goyawa mutanen Onuimo bisa ga noman shinkafa".

Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan

Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan
Source: Facebook

"Jam'iyar AA zata samar da ilimi kyauta a jihar Imo,zamu bada magani kyauta tun daga kan jinjiri zuwa dan shekara Bakwai,da kuma tsofaffi yan shekara 75 zuwa sama"

GA WANNAN: Kuyi magudi da APC kuyi bayani bayan zabe - PDP ta gargadi INEC

Dan takarar gwamnan ya kara fargar da mutane dasu kula matuka sannan ya shawarci matasa da mata dasu kula dasu kula da kuri'un su.

Nwosu yace "Karku bari su bata zaben,ku tabbatar da masu kula da akwatunan Ku ne suka irga kuri'un ku saboda wannan zabe yana da matukar muhimmanci a dimukradiyar mu,ku zabi jam'iyar AA sannan ku kiyaye ".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel