Yanzu-yanzu: Jirgin yakin neman zaben Buhari ya dira Jigawa

Yanzu-yanzu: Jirgin yakin neman zaben Buhari ya dira Jigawa

Shugaba Muhammadu Buhari da mambobin jam'iyyar All Progressives Congress sun iso jihar Jigawa a yau Asabar domin kaddamar da yakin neman zaben karo na biyu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewar jirgin shugaba Buhari ta baro jihar Gombe inda ta dako shugaban kasar da tawagarsa kuma da sauka a JIgawa misalin karfe 2.25 na rana.

NAN ta ruwaito cewa shugaban kasar ya fara ziyarar garin Barambu na karamar hukumar Alkaleri na jihar Bauchi inda ya rantsar da fara hako man fetur a rijiyan mai na Kolmani-ii, Gongola.

Yanzu-yanzu: Jirgin yakin neman zaben Buhari ta dira Jigawa

Yanzu-yanzu: Jirgin yakin neman zaben Buhari ta dira Jigawa
Source: UGC

DUBA WANNAN:

A yayin da ya ke kaddamar da fara hakar man fetur din, Shugaban kasa ya umurci hukumar NNPC ta fadada neman man fetur zuwa rijiyoyin ta shida da ke kasar.

Shugaban kasar kuma ya yi jawabi ga magoya bayan jam'iyya na APC a jihar Gombe bayan kaddamar da fara hakar man fetur din a Bauchi kafin ya taho Jigawa.

NAN ta ruwaito cewa dubban magoya bayan jam'iyyar APC sun cika titunan garin Dutse yayin da an rufe shagun da wuraren kasuwanci da dama domin tarbar shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel