Makarkashiya: Obasanjo ya sa labule da shugabannin jam'iyyu kwanaki kadan kafin zabe

Makarkashiya: Obasanjo ya sa labule da shugabannin jam'iyyu kwanaki kadan kafin zabe

Tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar ta Hudu, Cif Olusegun Obasanjo ya shiga wata tattaunawar sirri da shugabannin jam'iyyun adawa da ma mai mulki hade da na jami'an tsaro a gidan sa dake a jihar Ogun.

Wannan tattaunawar dai kamar yadda muka samu an soma ta ne da ranar Asabar, kwanaki kadan kafin zabukan gama-gari na shugaban kasar Najeriya, yan majalisun tarayya, gwamnoni da kuma 'yan majalisun jahohi.

Makarkashiya: Obasanjo ya sa labule da shugabannin jam'iyyu kwanaki kadan kafin zabe

Makarkashiya: Obasanjo ya sa labule da shugabannin jam'iyyu kwanaki kadan kafin zabe
Source: UGC

KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda tayi babban kamu a jihar Edo

Legit.ng Hausa ta samu cewa wasu daga cikin wadanda suka halarcin taron sirrin akwai Wale Egunleti, shugaban jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) na jihar Ogun, Gboyega Isiaka, dan takarar gwamnan jihar Ogun a jam'iyyar ta adawa African Democratic Congress (ADC).

Sauran sun hada da Chief Jide Ojuko, shugaban shiyya na jam'iyyar Allied Peoples Movement Campaign Council (APM) a jihar Ogun da kuma Ayo Olubori, Sakataren rikon kwarya na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar ta Ogun.

Haka zalika shima Mista Abimbola Oyeyemi, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ya samu halartar taron sirrin wanda aka ce shi tsohon shugaban kasar ne ya kira.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel