Rundunar 'yan sandan Najeriya tayi babban kamu a jihar Edo

Rundunar 'yan sandan Najeriya tayi babban kamu a jihar Edo

Rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Edo dake a yankin kudu maso kudancin Najeriya a ranar Juma'ar da ta gabata ta sanar da samun nasarar kubutar da akalla mutane 20 da akayi garkuwa da su a jihar cikin akalla sati biyu da suka gabata.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Mista Olusegun Odumosu shine ya bayyanawa manema labarai nasarar da suka samu a yayin wata tattaunawa da yayi da su a ofishin sa dake a hedikwatar 'yan sandan birnin Benin.

Rundunar 'yan sandan Najeriya tayi babban kamu a jihar Edo

Rundunar 'yan sandan Najeriya tayi babban kamu a jihar Edo
Source: Twitter

KU KARANTA: An tashi taron kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya baram-baram

Legit.ng Hausa ta samu cewa a cewar Kwamishinan, akalla mutane 83 ne dakarun su suka kama wadanda suke zargi da laifuffuka da dama da suka hada da shiga kungiyar asiri da kuma fashi da makami.

Haka zalika Mista Olusegun Odumosu ya kara da cewa jami'an sa sun kuma samu nasarar kama wasu mutane 11 da laifin kisan wani jami'in dan sandan su a garin na Benin karshen satin da ya gabata.

A wani labarin kuma Wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zaman ta a jihar Kano ta bai wa hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC damar kwace makudan kudaden ta fiye da N1bn daga hannun matar tsohon shugaban kasa Patience Jonathan.

Sanawar da hukumar ta EFCC ta fitar ranar Alhamis din da ta gabata ta ce mai shari'a Lewis Allagoa na babbar kotun tarayyar da ke Kano ne ya bai wa hukumar izinin kwace N1,000,494,000 da kamfanin Magel Resort Limited, wanda ke da alaka da matar tsohon shugaban kasar Patience Jonathan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel