Yanzunnan: Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin zabensa a jihar Abia cikin salo

Yanzunnan: Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin zabensa a jihar Abia cikin salo

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Asabar, 2 ga watan Fabreru, ya kaddamar da yakin zabensa a jihar Abia, inda ya nemi al'ummar jihar da su kad'a masa kuri'unsu a zaben mai zuwa, domin bashi damar zama shugaban kasar na gaba.

Atiku Abubakar, a shafinsa na Twitter, ya bayyana godiyarsa ga al'ummar jihar, bisa yadda suka fito kwansu da kwarkwatarsu wajen tarbarsa a lokacin da ya dira jihar, da kuma wadanda suka cika makil a filin da ya kaddamar da yakin zaben nasa.

Dan takarar shugaban kasar na PDP, ya sha alwashin samar da miliyoyin guraben ayyukan yi ga 'yan Nigeria, idan har ya samu nasarar lashe zaben mai zuwa, ya kuma dare kujerar shugabancin kasar.

KARANTA WANNAN: Yanzunnan: Dandanzon jama'a sun halarci kaddamar da yakin zaben Buhari a Gombe

Yanzunnan: Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin zabensa a jihar Abia cikin salo

Yanzunnan: Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin zabensa a jihar Abia cikin salo
Source: Twitter

A wani labarin kuwa; Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin zabensa a babban filin wasanni na Gombe, domin neman amincewar jama'ar jihar, akan kad'a masa kurinsu a zaben kujerar shugaban kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrerun da muke ciki.

Shugaban kasar, wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Yemi Osinbajo da kuma sauran jiga jigan jam'iyyar APC ya isa filin wasannin ne da misalin karfe 11:57 na safiyar Asabar, 2 ga watan Fabreru, 2019.

Hotunan yakin zaben Atiku a jihar Abia:

Peter Obi, abokin takarar Atiku Abubakar

Peter Obi, abokin takarar Atiku Abubakar
Source: Twitter

Dandazon matasa ke nuna goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar

Dandazon matasa ke nuna goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar
Source: Twitter

Jihar Abia: Dumbin jama'a sun halarci filin da Atiku ya kaddamar da yakin zabensa

Jihar Abia: Dumbin jama'a sun halarci filin da Atiku ya kaddamar da yakin zabensa
Source: Twitter

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel