Tsoro-ko-tsaro: Gwamna Ganduje ya sake kauracewa muhawarar 'yan takarar a Kano

Tsoro-ko-tsaro: Gwamna Ganduje ya sake kauracewa muhawarar 'yan takarar a Kano

Daya daga cikin yan takarkarin kujerar gwamnan jihar Kano na jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC), Abdullahi Umar Ganduje, ya sake kauracewa muhawarar da gidan watsa labarai na BBC Hausa ya gudanar a ranar Asabar.

Gwamna Ganduje dai dake zaman gwamna mai-ci a jihar ta Kano, yanzu haka kuma yana son a zaben shi karo na biyu a jihar mai yawan al'umma.

Tsoro-ko-tsaro: Gwamna Ganduje ya sake kauracewa muhawarar 'yan takarar a Kano

Tsoro-ko-tsaro: Gwamna Ganduje ya sake kauracewa muhawarar 'yan takarar a Kano
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Fasto da mabiyan sa sun shiga musulunci a jihar Kwara

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa BBC Hausa ta ce ta gayyaci Gwamnan Ganduje ne tare da wasu 'yan takara hudu domin tafka muhawara kan abubuwan da za su sanya a gaba idan suka lashe zaben gwamnan jihar kuma dukkan su sun halarta.

Gwamna Ganduje dai ya shiga bakin 'yan Najeriya a shekarar 2018 bayan wata jarida da ake wallafawa a intanet, Daily Nigerian, ta fito da wani bidiyo da ya nuna shi yana karbar abin da ake zargi cin hanci ne.

A bidiyon, an nuna gwamnan na Kano yana karbar damman daloli yana sanya wa a aljihu. Sai dai gwamnan ya sha musanta zargin.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan bayan ma Gwamnan ya kauracewa halartar wata muhawarar da kungiyoyin sa kai na jihar suka gudanar a tsakanin 'yan takarkarin gwamnan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel