Kungiyar Kananan hukumomin Najeriya sun zabi wanda suke so ya zama shugaban kasa a Mayu

Kungiyar Kananan hukumomin Najeriya sun zabi wanda suke so ya zama shugaban kasa a Mayu

- Kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta kasa ta bayyana goyon bayan ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kungiyar ta tabbatar da kasar nan bazata samu daidaituwa ba, ba tare da tallafin kananan hukumomi

- Shugaban kungiyar yace zasu jawo hankalin duk yan kungiyar a fadin kasar nan don tabbatar da shugaban ya koma kujerar shi

Kungiyar Kananan hukumomin Najeriya sun zabi wanda suke so ya zama shugaban kasa a Mayu

Kungiyar Kananan hukumomin Najeriya sun zabi wanda suke so ya zama shugaban kasa a Mayu
Source: UGC

Kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi, NULGE ta nuna goyon bayan ta akan takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugabancin kasa mai zuwa.

Shugaban kungiyar, Comrade Ibrahim Khaleel, wanda ya jagoranci wakilan kungiyar wajen taro da kungiyar tallafin Buhari, wanda shine shugaban kungiyar fadar shugaban kasa ta yaki da amfani da miyagun kwayoyi, Birgadiya janar Buba Marwa, a ranar litinin yace Buhari ya cancanci a goyi bayan shi saboda gaskiyar shi.

Yace shugaban kasar bai boye komai ba akan jajircewar shi na tabbatar da mulkin kananan gwamnati mai karfi a fadin kasar nan.

Ya tabbatar da cewa shugaban zai cika alkawurran shi idan aka zabe shi a ranar 16 game watan Fabrairu, wanda hakan yasa suma suke goyon bayan shi.

Comrade Jameel, wanda yace daidaituwar kasar nan bazata yuwu ba ba tare da an karfafa kananan hukumomi ba, yayi alkawarin zai jawo hankalin yan kungiyar a duk fadin kasar nan don tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

"Kamar yanda mukayi yarjejeniya, munyi namu iyakar. Zamu jawo hankalin yan kungiyar mu. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu goyon bayan mu, saboda muna da yakinin yana da rikon amana," inji shi.

Yace NULGE zata hada kai da kungiyoyin siyasa don hana lalacewar ta.

GA WANNAN: Ashe da gaske ne, camfin nan na satar banten mata yayi kamari a kudu, an kamo 19

A jawabin Birgadiya Janar Marwa mai ritaya, wanda shin tsohon shugaban gwamnatin jihar Legas, yayi alkawarin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yake tallafawa ma'aikata da sabbin dokoki na gari, zai rayuwa mai karko fiye da tsammani.

Tuni dama janar Marwa yayi kira game NULGE da ta goyi bayan gwamnatin tarayya don ganin kasar nan ta fita daga kangin miyagun kwayoyi ballantana matasa da mata.

Mutanen da suka samu halartar taron sun hada da tsohuwar mataimakiyar gwamnan filato, Mrs Pauline Tallen, Mrs Abike Dabiri-Erewa sai mashiryin kungiyar BSO, DR Mahmoud Mohammed.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel