Ranar da na bar PDP a ranar ta mutu murus! Inji Sanata Akpabio

Ranar da na bar PDP a ranar ta mutu murus! Inji Sanata Akpabio

- PDP ta dade da mutuwa a jihar Akwa Ibom, mun kuma birneta

- Akwai tabbacin cewa APC ce zata ci zabe a matakin tarayya da jiha

- Idan suka baku kudi, ku karba sai kuce su koma kauyen su

Ranar da na bar PDP a ranar ta mutu murus! Inji Sanata Akpabio

Ranar da na bar PDP a ranar ta mutu murus! Inji Sanata Akpabio
Source: Depositphotos

Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya jaddada cewa jam'iyyar APC ce zatayi nasara a zabe mai zuwa a matakin tarayya da jihar Akwa Ibom saboda jam'iyyar PDP ta dade da mutuwa a jihar inda su kuma suka binne ta.

GA WANNAN: Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar kare gajiyayyu, da ma kare kadarorin gwamnati

Sanata Akpabio ya sanar da hakan ne a yakin neman zaben a Abak, inda ya tabbatar da cewa sakamakon zabe zai yiwa gwamna Udom Emmanuel da mukarraban shi warwas, wanda yace zai nemi hanya mafi sauki don gujewa kaye.

Ranar da na bar PDP a ranar ta mutu murus! Inji Sanata Akpabio

Ranar da na bar PDP a ranar ta mutu murus! Inji Sanata Akpabio
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan ya zargi PDP da hayar bata gari don magudin zabe, amma kuma hakan ba zai tsorata APC ba saboda tuni ta fara murnar nasarar zabukan da za'ayi.

Yace:Ban taba ganin Dan da yafi mahaifin shi ba. Ni na sasu duk inda suke yanzu kuma nasan bazasu wuce ni ba. Ko daya daga cikin ku ya mori aiyukan ministocin su? Tun a ranar da na bar PDP, jam'iyyar ta mutu. A ranar 8 ga watan Augusta 2018, itace ranar da PDP ta mutu. Suna nan suna hayar yan bangar siyasa. Ina shawartar ku daku karbi kudin su amma kada kuyi abinda suke so."

Dan takarar kujerar gwamnan Akwa Ibom karkashin jam'iyyar APC, Obong Nsima Ekere, yayi godiya ga mutanen Abak sakamakon fitowar su kwai da kwarkwata don nuna goyon bayan su gareshi. Yace wannan yankin ne na farko da ya nuna goyon bayan shi gareshi tun a shekarar data gabata.

GA WANNAN: Yanzunnan: Jirgin da Osinbajo ke ciki ya fado kasa dazunnan a Kabba

Ekere yace a matsayin shi na tsohon manajan daraktan ofishin cigaban yankin Niger Delta, ya assasa yin wasu aiyukan cigaba a karamar hukumar, inda yace mutanen yankin na da yuwuwar mora daga romon mulkin shi idan aka zabe shi.

"Nayi aiyuka 11 a Abak kadai karkashin NDDC. Idan zan iya yin hakan, me kuke tunanin zanyi wa Abak idan na zama gwamna? Nazo ne saboda matasan mu su samu aikin yi, daliban mu su mora daga baitil malin mu, matanmu yan kasuwa su samu tallafi," inji shi.

Wannan gwamna Udom Emmanuel dake korafin babu kudi shine yanzu yake siyan mutane da kudi. Idan ya kawo kudi ku karba, sai ku fada mishi ya koma kauyen su."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel