Kuyi magudi da APC kuyi bayani bayan zabe - PDP ta gargadi INEC

Kuyi magudi da APC kuyi bayani bayan zabe - PDP ta gargadi INEC

- Jam'iyyar adawa ta PDP tace wa hukumar zabe inta isa tayi magudin zabe ta hanyar yan gudun hijira

- Shugaban jam'iyyar ta kasa yace hukumar zata fuskanci fushin yan Najeriya

- Atiku yace shine babbar gadar da zata sada manya da kanana a kasar nan

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Source: Depositphotos

Jam'iyyar adawa ta PDP tace wa hukumar zabe mai zaman kanta idan ta isa tayi magudin zabe ta hanyar amfani da yan gudun hijira.

Tace hukumar zaben zata fuskanci tsinuwar yan Najeriya.

Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, wanda yayi maganar a zagayen kamfen dinsu a Benin City, yace magudin zabe zai yiwa mutane mummunar illa saboda yanda zasu bayyana fushin su.

Yace idan aka zabi Alhaji, zai tseratar da kasar nan daga talauci, yunwa da kasar kashe.

"Kada hukumar zabe tayi amfani da yan gudun hijara wajen magudin zabe, In ba haka ba za a samu matsala"

Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP, ya kwatanta kanshi da gada tsakanin yara da manya, inda ya umarci mutane dasu zabe shi da kuma sauran yan takarar PDP.

GA WANNAN: Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar kare gajiyayyu, da ma kare kadarorin gwamnati

Ya hori matasan Najeriya dasu dage wajen kwato karagar mulkin kasar don cigaba.

Alhaji Abubakar ya roki yan Edo dasu tsare duk wasu abubuwan da zasu iya musu ra'ayi ko ayi amfani dasu don canza sakamakon zabe.

Abubakar yayi alkawarin juyo da kundin siyasa da tattalin arzikin kasar nan don gyara Najeriyar da yayanmu zasu mora ba tare da yunwa, rashin aikin yi, kashe kashe, rashin tsaro da sauran hargitsi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace tushen matsalar da kasar nan take ciki na da nasaba da jam'iyyar APC karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Abubakar yace habaka kanana, matsakaita ba manyan kasuwanci ita ce hanyar cigaba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel