Da duminsa: Hadimin gwamnan Rivers da aka sace ya kubuta

Da duminsa: Hadimin gwamnan Rivers da aka sace ya kubuta

- Babban mashawarcin gwamnan jihar Rivers akan filaye da safiyo, Mr Anugbom Onuoha, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane da suka sace shi

- A halin yanzu, Mr Onuoha na kwance a gadon asibiti, domin duba lafiyarsa

- Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa an yi garkuwa da Mr Onuoha a ranar 28 ga watan Janairu, 2019, inda aka kaishi wani waje da ba a sani ba

Babban mashawarcin gwamnan jihar Rivers akan filaye da safiyo, Mr Anugbom Onuoha, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane da suka sace shi.

Ya samu 'yancinsa ne a safiyar ranar Asabar, bayan da hadakar jami'an tsaro a jihar suka yi hobbosa wajen ganin sun kubutar da shi, inda a yanzu haka yake kwance a gadon asibiti, domin duba lafiyarsa.

An yi garkuwa da Mr Onuoha a ranar 28 ga watan Janairu, 2019, inda aka kaishi wani waje da ba a sani ba.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Buhari ya kaddamar da hakar man fetur a tsakanin Bauchi da Gombe

Da duminsa: Hadimin gwamnan Rivers da aka sace ya kubuta

Da duminsa: Hadimin gwamnan Rivers da aka sace ya kubuta
Source: Depositphotos

A wani labarin kuwa, rundunar 'yan sanda na ci gaba da farautar wadanda suka yi garkuwa da hadimin gwamnan. Rundunar ta sha alwashin gurfanar da duk wanda ta kama da hannu a ciki domin fuskantar shari'a.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar na jihar, Mr Omoni Nnamdi, ya roki daukacin al'ummar jihar da su ci gaba da dora kyakkyawan yakini akan rundunar, a yunkurinta na wanzar da zaman lafiya, musamman a yayin da ake fuskantar zabe mai zuwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel