Da duminsa: Shugaban APC a Adamawa da aka sace ya samu 'yanci yanzu

Da duminsa: Shugaban APC a Adamawa da aka sace ya samu 'yanci yanzu

Rahotannin da Legit.ng ta samu yanzu na nuni da cewa masu garkuwa da mutane, sun sako shugaban jam'iyyar APC na jihar Gombe, wanda suka sace awanni 11 kafin zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari kaddamar da yakin zabensa a jihar. A yanzu dai shugaban jam'iyyar ya na tare da iyalinsa cikin koshin lafiya.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC a jihar Gombe, Mohammed Abdullahi ya tabbatar da cewa shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Demsa da wasu masu garkuwa da mutane suka sace ya samu 'yanci a yanzu.

Idan za a iya tunawa, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa an sace Hamisu Mijinyawa ne a makon da ya gabata inda aka kaishi wani boyayyen waje, daga bisani kuma wadanda suka yi garkuwa da shi sun bukaci N20m a matsayin kudin fansarsa.

KARANTA WANNAN: Daga karshe: INEC ta yi tsokaci kan zuwan gwamnonin jamhuriyyar Niger Kano

Da duminsa: Shugaban APC a Adamawa da aka sace ya samu 'yanci yanzu

Da duminsa: Shugaban APC a Adamawa da aka sace ya samu 'yanci yanzu
Source: Twitter

Wata majiya ta tabbatar da cewa a halin yanzu dai, Hamisu na garinsa na Dmesa, tare da iyalansa cikin koshin lafiya.

Garkuwa da shugaban jam'iyyar na Demsa, ya zo ne awanni kadan kafin zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari kaddamar da yakin zabensa a jihar domin fuskantar zaben 2019 da zai gudana a cikin wannan watan na Fabreru.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel