Daga karshe: INEC ta yi tsokaci kan zuwan gwamnonin jamhuriyyar Niger Kano

Daga karshe: INEC ta yi tsokaci kan zuwan gwamnonin jamhuriyyar Niger Kano

- INEC ta ce zuwan wasu gwamnonin kasar Niger filin kaddamar da yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano bai sabawa wata dokar kasa ba

- Zuwan gwamnonin yakin zaben ya haddasa cece kuce a tsakanin 'yan Nigeria da ke zargin cewa an shigo da bakin haure kasar domin tafka magudi a zabe mai zuwa

- INEC ta ce ba ta da karfin iko na soke sunan wani dan takara, musamman shi Buhari da PDP ta ke magana akanshi, kotu ce kadai za ta iya yin hakan

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce zuwan wasu gwamnonin kasar Niger filin kaddamar da yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano bai sabawa wata dokar kasa ba.

INEC ta bayyana hakan a lokacin da take amsa tambayoyi kan wannan lamari.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa gwamnoni biyu daga jamhuriyyar Niger, na daga cikin wadanda suka halarci kaddamar da yakin zaben Buharin a jihar Kano

Zuwan gwamnonin yakin zaben ya haddasa cece kuce a tsakanin 'yan Nigeria da ke zargin cewa an shigo da bakin haure kasar domin tafka magudi a zabe mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: PDP ta bukaci INEC ta haramtawa Buhari shiga zaben 16 ga watan Fabreru

Daga karshe: EFCC ta yi tsokaci kan zuwan gwamnonin jamhuriyyar Niger Kano

Daga karshe: EFCC ta yi tsokaci kan zuwan gwamnonin jamhuriyyar Niger Kano
Source: UGC

Uche Secundus, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, a lokacin kaddamar da yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar, a jihar Enugu da ya gudana a ranar Juma'a, ya bukaci INEC da ta cire sunan Buhari daga cikin 'yan takarar shugaban kasa na zabe mai zuwa.

Ya yi zargin cewa shugaban kasa Buhari ya kawo bakin haure daga kasashen waje domin murde zaben mai zuwa da nufin bashi nasara, a lokacin da ya kaddamar da yakin zabensa na jihar Kano.

Sai dai a zantawarsa da jaridar TheCable, Oluwole Osaze-Uzzi, daraktan ilimantar da masu kada kuri'a da kuma harkokin hulda da jama'a na hukumar INEC, ya ce zuwan gwamnonin biyu jihar Kano bai sabawa wata doka ta kasa ba.

Ya ce doka dai kawai ta haramtawa wasu baki daga kasashen waje tsoma hannu a harkokin gudanar da zaben kasar.

Ya kuma ce hukumar ba ta da wani karfin iko na soke sunan wani dan takara, musamman shi Buhari da PDP ta ke magana akanshi, yana mai cewa kotu ce kadai za ta iya yin hakan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel