Dakarun Soji sun kama 'yan kungiyar IPOB a jihar Abia

Dakarun Soji sun kama 'yan kungiyar IPOB a jihar Abia

Dakarun sojojin Najeriya na 14 Brigade da ke Barikin Sojoji na Goodluck Jonathan a Ohafia a jihar Abia sun kama 'yan haramtaciyar kungiyar fafutikan kafa Biafra , IPOB a garin Aba.

Anyi ikirarin cewa 'yan kungiyar ta IPOB suna daga cikin wadansu matasa masu goyon bayan kafa Biafra da suka kai hari Cocin Katolika na St Mary a Abayi, Ariaria a karamar hukumar Osisioma a ranar 27 ga watan Janairu.

Punch ta ruwaito cewar an samu rudani a cocin ne bayan wasu 'yan IPOB din sun hana wani dan siyasa yin jawabi a cikin cocin.

Sojoji sun kama 'yan kungiyar IPOB a jihar Abia

Sojoji sun kama 'yan kungiyar IPOB a jihar Abia
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun halaka direba a hanyar Birnin Gwari

Wadanda abin ya faru a idanunsu sun ce limamin cocin Rabaran Fada Nathaniel Oyedike ya yi yunkurin kwantar da hankulan mutane a cocin amma mambobin IPOB din suka fara rera wakokin kafa Biyafara hakan yasa aka tashi ba shiri.

An gano cewar 'yan kungiyar ta IPOB sun ce sun gwammace ayi zaben jin ra'ayi a kan cigaba da kasancewarsu a Najeriya a maimakon gudanar da zabe a jihar Abia da wasu jihohin Kudu maso Gabas.

Daga baya sun fita harabar cocin inda suka lalata wata mota kirar Toyota Sienna mai dauke da tambarin jam'iyyar PDP da hoton Sanata mai wakiltan Abia ta Tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar, Theodore Orji.

Wata majiya daga 14 Brigade na Sojin ta tabbatar da cewa sojojin tare da hadin gwiwa da 'yan sanda sun kama wadansu masu goyon bayan Biafra domin tabbatar da tsaro a garin.

Majiyar da ta nemi a boye sunanta ta ce, "'yan kungiyar ta IPOB suna ta ihun cewa ba za ayi zabe a Biafra ba kuma sunyi yunkurin yiwa Rabaran Fada Nathaniel Oyedike duka. An kuma lalata wasu kujeru da mota a harabar cocin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel