Jiki magayi: EFCC ta gargadi bankuna kan karbar kudaden haramun daga hannun 'yan siyasa

Jiki magayi: EFCC ta gargadi bankuna kan karbar kudaden haramun daga hannun 'yan siyasa

- Ibrahim Magu, ya yi kira ga bankuna na kasar da su kauracewa karbar kudaden haramun daga hannun bata garin 'yan siyasa da kuma 'yan ta'adda

- Ya ce da yawa daga cikin wadanda suka sace kudaden kasar, sun fara dawowa da su kasar domin sayen kuri'u da kuma sayen imanin jami'an gudanar da zabe

- Shugaban EFCC sai kuma ya bukaci mambobin kungiyar da su hada hannu da hukumar domin tabbatar da cewa ba a samu tangarda a zabe mai zuwa ba

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya yi kira ga bankuna da kuma manyan cibiyoyin adanawa da raba kudade na kasar da su kauracewa karbar kudaden haramun daga hannun bata garin 'yan siyasa da suka kware wajen rashawa da kuma 'yan ta'adda.

Magu ya bayyana wannan bukatar ne a wani babban taro na kungiyar manyan jami'an bankuna na Nigeria, ACCOBIN, wanda ya gudana a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu, 2019 a garin Legas.

Ya ce da yawa daga cikin wadanda suka sace kudaden kasar, sun fara safararsu zuwa cikin kasar a dai dai wannan lokaci, domin yin amfani da su wajen sayen kuri'u da kuma sayen imanin jami'an gudanar da zabe.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Al'ummar Ijaw sun yi tattaki a Abuja domin nuna goyon bayansu ga Buhari

Jiki magayi: EFCC ta gargadi bankuna kan karbar kudaden haramun daga hannun 'yan siyasa

Jiki magayi: EFCC ta gargadi bankuna kan karbar kudaden haramun daga hannun 'yan siyasa
Source: UGC

Shugaban hukumar EFCC sai kuma ya bukaci mambobin kungiyar da su hada hannu da hukumar yaki da cin hanci da rashawa domin tabbatar da cewa ba a samu tangarda a zabe mai zuwa ba, yana mai cewa idan har aka samu matsala a zaben, to Allah kadai ya san irin mummunar matsalar da zai haddasa.

Ya ce: "Hakika akwai nauyin da ya rataya a wuyan kowannenmu, kuma ya zamar mana wajibi mu sauke wannan nauyi kamar yadda ya kamata ta hanyar bin doka da odar da gwamnati ta kafa kan zabuka."

Ya kara da cewa sayen kuri'un jama'a yanzu ya canja salo, inda ake masa lakabi daban daban da sunan shirin bunkasa jama'a, kamar misalin "shirin a kori yunwa", "shirin bunkasa rayuwa", "shirin bayar da bashin kudin da babu riba" da kuma "bayar da tallafin tsabar kudi ga mabukata", da dai sauransu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel