Wani Fasto da mabiyan sa 14 sun karbi musulunci a jihar Kwara

Wani Fasto da mabiyan sa 14 sun karbi musulunci a jihar Kwara

Wani labari da muka samu daga majiyar mu ta Nairaland ya bayyana cewa wasu mabiya addinin kirista su akalla 15 cikin su hadda Fasto da suka karbi addinin muslunci a garin Ilori na jihar Kwara dake a shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Wani mai anfani da kafar sadarwar zamani na Tuwita ne da ke da adreshin Dahwah007 dai ya labarta hakan inda kuma yace kungiyar dake gwagwarmayar jawo hankalin mutane zuwa ga addinin muslunci mai suna Academy for Islamic propagation (ACADIP) ce ta jagoranci musuluntar da bayin Allahn.

Wani Fasto da mabiyan sa 14 sun karbi musulunci a jihar Kwara

Wani Fasto da mabiyan sa 14 sun karbi musulunci a jihar Kwara
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An tashi baram-baram a taron ASUU da gwamnatin tarayya

Sannan kuma Dahwah007 ya kara da cewa kimanin kiristoci 316 ne dai suka karbi musulunci a cikin watanni 6 da suka wuce a jihar.

Fatan mu shine Allah ya karbi tubar su ya kuma sa muma mu mutu muna musulmai. Amin.

A wani labarin kuma, gamayyar kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya watau Christian Association Nigeria (CAN) a takaice sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wa'azi mai ratsa zuciya game da zabukan gama gari da ake shirin gudanarwa da dukkan fadin kasar nan da 'yan kwanaki.

Kungiyar wadda ta yi masa wa'azain a cikin wata takardar matsaya da ta fitar bayan taron ta na lokaci-zuwa-lokaci da ta gudanar a garin Abuja, tace ya kamata ya san girman alkawari ya tabbatar da gudanar da sahihin zabe domin kaucewa rikici da zubda jini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel