Yanzu-Yanzu: An tashi baram-baram a taron tattaunawar ASUU da gwamnatin tarayya

Yanzu-Yanzu: An tashi baram-baram a taron tattaunawar ASUU da gwamnatin tarayya

A yau ma kamar sauran ranakun baya, tattaunawa a tsakanin jami'an gwamnatin tarayya da kuma kungiyar malaman makarantun Najeriya watau Academic Staff Unioun of Universities (ASUU) ya tashi baram-baram ba tare da cimma matsaya ba.

Mun samu dai cewa shugaban kungiyar ASUU jim kadan bayan kammala tattaunawar, ya ce ba'a cimma matsaya ba kuma za'a cigaba da tattaunawar a ranar Alhamis mai zuwa 7 ga watan Fabreru.

Yanzu-Yanzu: An tashi baram-baram a taron tattaunawar ASUU da gwamnatin tarayya

Yanzu-Yanzu: An tashi baram-baram a taron tattaunawar ASUU da gwamnatin tarayya
Source: UGC

KU KARANTA: Gobara ta yi mummunar barna a jihar Kano

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa shima ministan kwadago Dakta Chris Ngige da yake zantawa da manema lanarai, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu dai gwamnatin tarayya bata da Naira biliyan 50 da za ta saka a cikin harkar ilimin jami'o'i kamar yadda kungiyar ta ASUU ke bukata.

Idan mai karatu bai manta ba dai zai tuna cewa mun kawo maku labarin cewa kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU sun shiga ganawar sirri da wakilan gwamnatin tarayya a babban birnin tarayya Abuja da farkon daren yau.

Kamar dai yadda muka saida maku, , taron dai an kira shi ne cikin gaggawa.

Idan ba a manta ba, kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki a cikin watan Nuwamba, 2018 domin nuna rashin amincewarsu akan kudaden da ake turawa jami'o'in, da kuma gazawar gwamnati na cika alkawuran da ta daukar masu, da dai sauran wasu dalilai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel