Matsafa sun cire sassan jikin wasu mata da suka kashe bayan sunyi masu fyade

Matsafa sun cire sassan jikin wasu mata da suka kashe bayan sunyi masu fyade

An yiwa wasu mata biyu kisar gilla a garin Akenfa da ke kan iyakar Yenagoa a jihar Bayelsa sannan matsafar da ake zaton sun kashe su sun cire wassu sassan jikinsu.

Kisan ya faru ne a lokuta daban-daban a garin na Akenfa kuma hakan ya jefa al'ummar garin cikin rudani da fargaba.

An tsinci gawar wata Glory Omo-Ohwo 'yar asalin jihar Delta mai sana'ar sayar da kifi da alamun anyi mata fyade sannan aka fasa kanta kuma aka jefar da gawarta a wani kangon gini a ranar Laraba.

Matsafa sun cire sassan jikin wasu mata da suka kashe bayan sunyi masu fyade

Matsafa sun cire sassan jikin wasu mata da suka kashe bayan sunyi masu fyade
Source: Twitter

Wannan ya faru ne kwanaki hudu bayan an yiwa wata mahaifiyar yara hudu mummunan kisa har ta kai ga ba a gane fuskatar kuma an kwakwule kwakwalwarta.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun halaka direba a hanyar Birnin Gwari

An gano cewa Omo-Ohwo ta farka ne misalin karfe 5 na asubahin ranar Talata 29 ga watan Janairun 2019 domin ta fara gasa kifin da ta sayo.

Sai dai yaranta sun farko ba su ganta ba sai dai warin takalminta guda daya. Daga bisani an gano gawarta a wani kangon gini da ke kusa da gidan da ta ke zaune kuma an kwakwule mata kwakwalwa.

An kuma tsinci gawar wata mace mai sayar da meat-pie, Goodnews Stephen wadda 'yar asalin karamar hukumar Kolokumo/Opokuma ne da ke jihar Bayelsa. An tsinci gawarta a safiyar ranar Juma'a itama babu kwakwalwarta.

An tsinci gawarta ne a bayan makarantar sakandire ta Akanfa.

Da aka tuntube shi, Kakakin 'yan sandan jihar, Asinim Butswat ya ce ya samu labarin afkuwar kisar kuma tuni rundunar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel