EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

Wani jami'in EFCC, Mahmud Tukur ya shaidawa Mai shari'a Lewis Allagoa na babban kotun jihar Kano yadda bincike ya tona yadda tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau da wasu mutane biyu suka hada baki suka karbi rashawar Naira miliyan 950 daga Bankin Fidelity.

An gurfanar da Shekarau ne a kotu tare da Aminu Bashir Wali da Mansur Ahmed inda ake tuhumarsu da aikata laifuka shida masu alaka da hadin baki da karkatar da kudi wanda yawansu ya kai Naira Miliyan 950.

Anyi ikirarin cewar kudin da suka karba yana daga cikin kudin haramun da tsohuwar Ministan Man Fetur, Diezani Alison-Madueke ta wawushe ne domin kamfen a babban zaben 2015.

Lauyan EFCC, Samuel Chime ya gabatar da jawabin da shaidun uku su kayi yayin da ake musu tambayoyi a matsayin hujja a kotun.

An kuma gabatarwa kotun wasika daga Bankin Fidelity a matsayin hujja na zargin.

EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m
Source: Twitter

Mr Tukur, wanda ya bayar da shaida ya ce a cikin kudin, an raba ma wasu 'yan jam'iyyar PDP a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

Ya ce: "Bayan kammala binciken an gano cewar Wali da Mansur sun karbi N950 miliyan daga Bankin Fidelity da ke Murtala Mohammed Way a ranar 9 ga watan Maris na 2015 sannan suka mikawa babban hadimin Shekarau inda ya daga bisani Shekarau ya bayar da umurnin a kai kudin gidansa sannan aka raba kudin a ranar 27 ga watan Maris na 2015."

Ya ce karbar irin wannan zunzurutun kudin da rabar da ita ya sabawa dokar karkatar da kudi na kasa.

Mr Tukur ya shaidawa kotu cewa Mr Shekarau ya samu N25 miliyan cikin kudin yayin da Wali ya samu N25 miliyan shi kuma Mansur ya samu N10 miliyan.

Lauyan EFCC kuma ya kira shaidansa na biyu, tsohon ma'aikacin Fidelity Bank reshen Murtala Mohammed Way a jihar Kano, Saheed Adeolula.

Mr Adeolula ya shaidawa kotu cewa an watan Maris na 2015 an kira shi daga hedkwata an umurci ya fitar da N950 miliyan ya mikawa Wali wadda ya taho tare da Mansur.

Ya ce kafin ya biya kudin sai da ya sake kiran hedkwatan ya tabbatar kafin ya biya kudin.

"Mun tafi CBN domin samo kudi saboda ba mu da isashen kudi a wurin mu hakan ya dan kawo tsaika, daga bisani cikin dare aka kammala biyan kudin," inji shi.

Adeolula ya shaidawa kotu cewa an biya kudin ne ba ta yadda aka saba biya a bankin ba.

An dage cigaba da sauroron shari'ar zuwa ranar 10 da 11 na watan Afrilun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel