Wani saurayi ya halaka budurwarsa bayan ya damfareta N500,000

Wani saurayi ya halaka budurwarsa bayan ya damfareta N500,000

Rundunar Yansandan jahar Ogun ta sanar da kama wani mutumi mai shekaru 47, Kazeem Adebayo da laifin kashe budurwarsa mai shekaru 30, Abosede Adesanya akan kudi naira dubu dari biyar da talatin, N530,00, sa’annan ya binneta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda sun kama Kazeem ne bayan mahaifiyar Abosede, Amoke Onasanya ta kai musu rahoto a ofishinsu dake Ijebu-Igbo, inda ta bayyana musu cewa diyarta na gida saurayinta ya kirata a waya.

KU KARANTA; Yakin neman zabe: Babu bukatar Buhari ya je Zamfara – Sanata Kabiru Marafa

Mahaifiyar tace a lokacin da saurayin ya kirata ya yi mata tallar wani fili ne, wanda hakan yasa ta kai masa kudi N530,000 da nufin sayen filin, sai dai jim kadan bayan fitanta sai suka dinga kiran lambar wayarta, amma bata shiga.

Cikin wata sanarwa da kaakakin Yansandan jahar, Abimbola Oyeyemi ya fitar a ranar Juma’a, 1 ga watan Feburairu a garin Abekuta na jahar Ogun yace bayan sun kama mutumin sun kaddamar da bincike akansa, sai ya garzaya dasu makabartar daya binne budurwar tasa.

“Ya bayyana mana gaskiyar cewa shine ya kashe budurwar tasa ta hanyar amfani da kota, daga nan ya binneta da a cikin wani makabarta a cikin gidansa, sa’annan ya fada mana cewa ya yi amfani da N30,000 daga cikin kudin don biyan bashi, yayin daya baiwa wani abokinsa ajiyan N500,000.” Inji Oyeyemi.

Daga karshe kaakakin Yansandan ya bayyana cewa zuwa yanzu sun mika gawar matar zuwa dakin ajiyan gawarwaki dake babban asibitin garin Abekuta na jahar Ogun don gudanar da binciken kwakwaf.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel