Labari mai dadi: Buhari zai kaddamar da hakar man fetir a jahar Gombe

Labari mai dadi: Buhari zai kaddamar da hakar man fetir a jahar Gombe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da fara hakan man fetir a jahar Gombe a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu, wanda hakan zai shigar da jahar Gombe cikin jerin kasashen Najeriya dake da arzikin man fetir.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari zai kaddamar da hakan man ne a yankin tafkin Kolmani, wani sashi dake tsakanin jahar Gombe da jahar Bauchi, kamar yadda hukumar man fetir na Najeriya, NNPC ta sanar.

KU KARANTA: Yakin neman zabe: Babu bukatar Buhari ya je Zamfara – Sanata Kabiru Marafa

Labari mai dadi: Buhari zai kaddamar da hakar man fetir a jahar Gombe

Buhari
Source: UGC

Babban manajan watsa labaru na hukumar NNPC, Ndu Ughamadu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu, inda yace shugaba Buhari zai kaddamar da aikin ne tare da hadin gwiwar shugaban NNPC, Maikanti Baru.

Yankin da za’a kaddamar da hakan man fetir din, tafkin Kolmani II, yana kusa da kauyen Barambu dake cikin karamar hukumar Alkaleri na jahar Bauchi, haka zalika Mista Ndu yace an soma hakan man fetir dinne sakamakon wasu sabbin dabaru da shugaban NNPC, Maikanti ya zo dasu.

Makasudin samar da wadannan dabaru shine domin kara adadin danyen mai da iskar gas da Najeriya take fitarwa, samar da isashshen man fetir a Najeriya, samar da karin kudin shiga ga gwamnati da kuma samun karin wuraren hako mai a yankin Arewa.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai isa jahar Gombe a ranar Asabar, 1, ga watan Feburairu domin cigaba da yakin neman zabensa na takarar shugaban kasa a karo na biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel