Da duminsa: Sarkin yakin neman zaben PDP ya koma APC

Da duminsa: Sarkin yakin neman zaben PDP ya koma APC

Direkta Janar na yakin neman zaben jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Gombe ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar.

Sanarwar data fito daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya ce Bala Bello Tinka wanda akafi sani da Tinka Point ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a daren Alhamis.

Mr Adesina ya ce a wurin taron, Mr Tinka ya yi alkawarin yiwa APC aiki kuma ya lashi takobin yin amfani da matsayinsa na siyasa domin ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zabe domin zarcewa karo na biyu.

Da duminsa: Sarkin yakin neman zaben PDP ya koma APC

Da duminsa: Sarkin yakin neman zaben PDP ya koma APC
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

"A yanzu da ake makonni biyu kafin babban zabe, ficewar Alhaji Tinka daga PDP reshen jihar Gombe ya yiwa jam'iyyar babban ila. PDP ne ke mulki a jihar kuma su ke mulki tun shekarar 2003," inji Adesina.

"Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kamfen a jihar Gombe ranar Asabar inda ake sa ran Alhaji Tika sai sanar da komarsa APC tare da wasu mutanen a wurin taron."

Mr Tinka ya so ya yi takarar gwamna a jihar ta Gombe domin maye gurbin Ibrahim Dankwambo amma bai yi nasarar samun tikitin takara na jam'iyyar ta PDP ba.

Tinka babban dan kasuwa ne kuma dan kwangila a jihar Gombe. Shi ya ke da kamfanin Tinka Point Limited wadda ya kafa tun shekarar 1986.

Alhaji Tinka kuma na hannun daman Gwamna Dankwambo ne amma ba a san dalilin da yasa ya fice daga PDP ba.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta kawo ruwaito muku cewa tsohon sakataren gwamnatin, Mainasara Sajo, Ciyamomin karamar hukuma 10 da wasu mutane 3,510 'yan jam'iyyar APC a karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi sun koma jam'iyyar PDP.

Sajo, wanda sakataren gwamnati ne yayin mulkin Saidu Dakingari ya sanar da komawarsa PDP na a wurin kamfen da aka gudanar a jihar na dan takarar gwamna Isa Galaudu a ranar Alhamis 31 ga watan Janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel