'Yan bindiga sun halaka direba a hanyar Birnin Gwari

'Yan bindiga sun halaka direba a hanyar Birnin Gwari

A safiyar yau Juma'a ne wasu 'yan bindiga suka bude ma wata motar fasinja wuta a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna inda suka kashe direban motan nan take.

Harsashin da suka harba ya sami direban, Muhammadu Lawal Suleiman a kansa hakan yasa ya ce ga garinku a nan take.

Lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Unguwar Yako da kusa da garin Udawa misalin karfe 7 na safiya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daya daga cikin fasinjojin motar da ya nemi a boye sunansa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa yana zaune a gaban motar lokacin da 'yan bindigan suka budewa motar wuta.

'Yan bindiga sun kashe wani direba a titin Birnin Gwari

'Yan bindiga sun kashe wani direba a titin Birnin Gwari
Source: UGC

DUBA WANNAN: Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

"Mu 10 ne a cikin Gulf 3 muna hanyar mu ta zuwa Kano sai kwatsam muka ji karar bindiga. Sun bude wa motar mu wuta kuma daya daga cikin harsashin ya samu direban a kai. Bamu san an harbe shi ba sai bayan da motar da tsaya a cikin daji kuma dukkan mu muka fito domin mu tsira da ran mu," inji shi.

Ya ce 'yan bindigan sun kai su bakwai kuma dukkansu na dauke da muggan bindigogi.

An gano cewar an yiwa direban da rasu jana'iza a kauyen Udawa.

Wani shugaban 'yan kato da gora a kauyen Udawa, Hussaini shime ya tabbatar da cewar an yiwa direban sallar kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

An tuntubi Kakakin 'yan sanda na jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo domin jin ta bakinsa amma wayarsa a kashe ta ke kuma bai amsa sakon tes da aka yi masa ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel