Dakarun Soji sun kashe 'yan Boko Haram 5 a Borno

Dakarun Soji sun kashe 'yan Boko Haram 5 a Borno

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarun bataliyyar 192, sector 1 na Operation Lafiya Dole sun kashe mayakan Boko Haram guda biyar.

Mai magana da yawun rundunar Operation Lafiya Dole 7 Division Sector 1, Kwanel Ado Isa ne ya bayar da sanarwar a cikin wata sako da ya fitar a ranar Alhamis.

A cewar Kwanel Isa, dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'addan hudu ne a yayin da suke sintiri tare da Civilian JTF a hanyar Gwoza zuwa Yamtekeon a ranar Laraba.

Dakarun Soji sun kashe 'yan Boko Haram 5 a Borno

Dakarun Soji sun kashe 'yan Boko Haram 5 a Borno
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan PDP fiye da 3,500 sun dunguma sun koma APC a Delta

Kakakin rundunar sojin ya ce daya daga cikin 'yan ta'addar wani gawurtaccen dan ta'ada ne mai suna Adamu Rugu da ya yi kaurin suna a yankin Gwoza a jihar Borno.

A wani labari mai kama da wannan, dakarun bataliyyar 152 na Operation Lafiya Dole sun yiwa wasu 'yan ta'adda kwantar bauna a kan titin Kumshe zuwa Usman Road.

A harin da suka kai musu, dakarun sojin sun sake kashe wani dan ta'addan kungiyar Boko Haram guda yayin da wasu guda biyu suka tsere da raunin harsashi.

Har ila yau, dakarun bataliyar 195 na Operation Lafiya Dole tare da hadin gwiwar Civilian JTF da 'yan sanda suma sun damke wani dan ta'ada mai suna Mohammed Maina.

An kama shi dauke da kayan sojoji da na 'yan sanda daga bisani an mika shi zuwa ga sashin binciken bayyanan sirri domin su cigaba da bincike a kansa.

An kuma kwato bindiga guda biyu kirar AK-47 daga hannunsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel