Yanzu Yanzu: Buhari ya dage gangamin kamfen dinsa a Zamfara

Yanzu Yanzu: Buhari ya dage gangamin kamfen dinsa a Zamfara

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage gangamin kamfen dinsa na jihar Zamfara

- Shugaban kasar ya soke shirin ziyarar nasa zuwa Zamfara saboda rikicin siyasa da ke gudana yanzu haka a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage gangamin kamfen dinsa na jihar Zamfara wanda aka shirya gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairun 2019.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban kasar ya soke shirin ziyarar nasa zuwa Zamfara saboda rikicin siyasa da ke gudana yanzu haka a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar.

Yanzu Yanzu: Buhari ya dage gangamin kamfen dinsa a Zamfara

Yanzu Yanzu: Buhari ya dage gangamin kamfen dinsa a Zamfara
Source: UGC

Sunayen yan takara na APC bayan cikin jerin sunayen yan takarar zaben gwamna da na majalisar dokokin jiha da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saki a yau.

KU KARANTA KUMA: Da Buhari ya sa hannu a kudirin gyaran dokar zabe – El-Rufai

A halin da ake ciki, mun ji cewa duk da hukuncin da hukumar zabe mai zaman kantan (INEC) ta yanke a daren ranar Laraba na hana APC gabatar da yan takara daga jihar Zamfara, jam’iyyar All Progressives Congress tace ba ma a jihar Zamfara kadai ba harda jihar Rivers sai ta cike yan takara.

Babban sakataren labarai na jam’iyyar na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana hakan a jiya Alhamis, 31 ga watan Janairu a Abuja, jaridar Vanguard ta ruwwaito.

Yayi ikirarin cewa jamiyyar adawa ta Peoples Democratic Party ba ta gudanar da zaben fidda gwani ba a jihar Kano kuma INEC ba ta yi watsi da yan takararsu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel