Ba wanda zai kashe yanar gizo a lokutan zabe hukumar tsaro ta NSA ta fadi

Ba wanda zai kashe yanar gizo a lokutan zabe hukumar tsaro ta NSA ta fadi

- An zargi wai NSA zata hana ganin lissafin zabe a lokutan zabe

- NSA ce mai kula da tsaron cikin gida

- Ta karyata, tace baya cikin tsarinta

Ba wanda zai kashe yanar gizo a lokutan zabe hukumar tsaro ta NSA ta fadi

Ba wanda zai kashe yanar gizo a lokutan zabe hukumar tsaro ta NSA ta fadi
Source: Depositphotos

Hukumar tsaron kasa ta NSA, wadda Dasuki ya jagoranta a baya, ta karyata zargin da wasu musamman daga bangaren PDp keyi cewa wai zata kashe harkar sadarwa a lokutan zabe, a koma kamar yadda ake a zamunnan da.

Wannan zargi, in gaskiya ne, yana nufin babu facebook, twitter, instagram, da ma labarun intanet masu kawo shi da zafinshi, wadda hakan ke nufi sai an rattaba hannu a zabukan, sannan 'yan Najeriya zasu bi, maimakon yadda ake yi kowa ya gano na unguwarsu ya saki don shaida.

GA WANNAN: 2019: Dalilan da yasa yankin Yarabawa baza su yi Atiku ba

A lokuta da dama a wasu kasashen haka ake yi, sai dai talakawa suyi ta Allah-ya-isa, domin kuwa babu wata hanya ta samun labaru sai ta bakin gwamnati, lamari dake kawo hargitsi kan maganar magudi.

NSA a baya, a 2014, lokacin Dasuki, ta hana ma zaben ne kwata-kwata, inda ta kaishi cikin Maris, sati shidda daga lokacin yinsa don a samu a dawo da tsaro. A wani bangare kuma, NSA din aka zarga da kokarin hana shugaba Buhari cin zaben saboda lokacin yayi farin jini.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel