Da Buhari ya sa hannu a kudirin gyaran dokar zabe – El-Rufai

Da Buhari ya sa hannu a kudirin gyaran dokar zabe – El-Rufai

- Daga karshe Gwamna Nasir El-Rufai yayi martani akan kin sanya hannu a dokar gyaran zabe da Shugaba Buhari ya ki yi

- El-Rufai yace da Shugaban kasar ya sani ya sanya hannu akan dokar zaben

- Gwamnan yace a nazarin da yayi babu wani takamaimen abin da ya sauya sabon kudirin dokar daga Dokar Zabe ta ainihi

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi martani a kar na farko kan kin sanya hannu a dokar gyaran zabe da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaki yi, inda ya bayyana cewa da Shugaban kasar ya sani, da ya sa wa sabon dokar zaben hannu.

El-Rufai ya yi wannan kalami ne a cikin wata hira da ya yi da Gidan Talbijin na Channels a makonni da suka wuce.

Da Buhari ya sa hannu a kudirin gyaran dokar zabe – El-Rufai

Da Buhari ya sa hannu a kudirin gyaran dokar zabe – El-Rufai
Source: Depositphotos

Gwamnan ya ce ya yi nazarin Sabon Kudirin Gyaran Dokar Zabe sosai, amma abin da ya fahimta, shi ne babu wani takamaimen abin da ya sauya sabon kudirin dokar daga Dokar Zabe ta ainihi.

KU KARANTA KUMA: PDP ta yi babban kamu a jihar Kebbi inda wani jigon APC da wasu 3,510 suka sauya sheka zuwa jam’iyyar

Gwamnan na Kaduna ya ce don Shugaban Kasa bai sa hannu a sabon kudirin dokar ba, hakan ba zai hana INEC tattara bayanan sakamakon zabe ta intanet ba, domin ita dokar zabe abu ce da za a iya fadada ma’anar ta.

Ya ce INEC za ta iya tattara bayanan sakamakon zabe ta hanyar intanet idan ta fadada ma’anar karfin ikon da Dokar Zabe ta bai wa hukumar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel