Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar kare gajiyayyu, da ma kare kadarorin gwamnati

Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar kare gajiyayyu, da ma kare kadarorin gwamnati

- Shugaban kasa Muhammadu buhari ya sa hannu a dokar cin zarafin masu gama da nakasa. Ita dai wannna doka tayi tsawon shekaru goma sha takwas a majalisa kafin a tabbatar da ita yanzu

- A sashe na 31 na dokar ya nuna za a kirkiro kungiyar masu fama da nakasa ta kasa kuma za a nada shugabanci mai inganci

- Itadai wannan doka tayi wa kungiyoyi da dama dadi musamman kungiyar masu yaki da batanci wanda suka zargi shugaba buhari da nuna halin ko in kula ga masu fama da nakasa

Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar kare gajiyayyu, da ma kare kadarorin gwamnati

Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar kare gajiyayyu, da ma kare kadarorin gwamnati
Source: UGC

Shugaban kasa Muhammadu buhari ya sa hannu a dokar cin zarafin masu gama da nakasa. Ita dai wannna doka tayi tsawon shekaru goma sha takwas a majalisa kafin a tabbatar da ita yanzu.

Jami'ar sadarwar shugaban kasa ta majaliar Itah Enang ce ta bayyana hakan a Daren larabar da ta gabata. Dokar dai ta ce duk Wanda aka kama da laifin cin zarafin masu fana da nakasa to tabbas zai fuskanci fushin hukuma.

Idan har aka kama mutun da laifin cin zarafin masu nakasa to zai biya tarar kudi naira dubu dari ko kuma ya shade tsawon wata shida a gidan maza. Dokar dai zatayi aiki a koina da ina Wanda ya hada da guraren tafiye tafiye da tashoshin jirgin kasa, sama da na ruwa

Masu fama da nakasar dai zasu samu cikakkiyar dama ta Ilmi, da lafiya kuma za a rinka basu kulawa ta musamman a lokacin da abun gaggawa ya taso. Sannan kuma za a rinka ware kaso biyar na mutanen da za a rinka dauka a kowani ma'aikata ga nakasassu. Hakazalika an basu damar shigar da karar duk Wanda ya ci zarafinsu ta hanyar karya wadannan dokokin da aka fitar saboda su.

A sashe na 31 na dokar ya nuna za a kirkiro kungiyar masu fama da nakasa ta kasa kuma za a nada shugabanci mai inganci.

GA WANNAN: PDPn Tambawal na can yana saye quri'un Sokoto - APC ga INEC Read more:

Itadai wannan doka an tabbatar da itane bayan kwana daya da shugaban kasa da mataimakin sa sukace su fa ba a kawo musu tsarin lissafin dokar daga majalisar ba amma majalisar ta musanta wannan maganar ta shugaban kasa inda sukace tun shekarar 2018 suka muka wannan tsarin doka ga shugaban kasar.

Itadai wannan doka tayi wa kungiyoyi da dama dadi musamman kungiyar masu yaki da batanci wanda suka zargi shugaba buhari da nuna halin ko in kula ga masu fama da nakasa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel