Yanzu yanzu: ASUU ta saka labule da jami'an gwamnatin tarayya a Abuja

Yanzu yanzu: ASUU ta saka labule da jami'an gwamnatin tarayya a Abuja

Rahoton da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU sun shiga ganawar sirri da wakilan gwamnatin tarayya a babban birnin tarayya Abuja, taron dai an kira shi ne cikin gaggawa.

Idan ba a manta ba, kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki a cikin watan Nuwamba, 2018 domin nuna rashin amincewarsu akan kudaden da ake turawa jami'o'in, da kuma gazawar gwamnati na cika alkawuran da ta daukar masu, da dai sauran wasu dalilai.

Taron dai na gudana ne a bayan labule.

Cikakken labarin yana zuwa...

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Al'ummar Ijaw sun yi tattaki a Abuja domin nuna goyon bayansu ga Buhari

Yanzu yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga ganawar sirri da jami'an gwamnatin tarayya

Yanzu yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga ganawar sirri da jami'an gwamnatin tarayya
Source: UGC

A wani labarin; Daruruwan matasan al'ummar Ijaw da ke zaune a jihohi 19 na Arewacin Nigeria da na birnin tarayya Abuja, suka mamaye babban ofishin shirin bayar da tallafi na shugaban kasa da ke Abuja domin gudanar da tattakin nuna goyon baya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mai taimakawa shugaban kasar ta fuskar farfado da Niger Delta, Farfesa Charles Dokubo.

Matasan da ke dauke da kwalaye masu rubutun bayyana goyon bayansu ga tazarcen shugaban kasa Buhari, sun gudanar da tattakin ne karkashin jagorancin shugaban kungiyar matasan Ijaw a Arewacin Nigeria, Comrade Akasah Eniyekeye Kelvin, wanda ya ce za su tabbata Buhari ya samu kuri'un su a zabe mai zuwa.

Akasah wanda ya ce kungiyar ta shirya gudanar da taron wayar da kan jama'a a Abuja domin bayyana mubayi'arsu ga tazarcen Buhari a hukumance, ya kara da cewa tuni shirye shirye suka yi nisa na gudanar da gangamin matasa akalla miliyan ukku na kungiyar a fadin kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

witter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel