Zaben 2019: Al'ummar Ijaw sun yi tattaki a Abuja domin nuna goyon bayansu ga Buhari

Zaben 2019: Al'ummar Ijaw sun yi tattaki a Abuja domin nuna goyon bayansu ga Buhari

- Daruruwan matasan al'ummar Ijaw da ke zaune a jihohi 19 na Arewacin Nigeria suka mamaye babban ofishin shirin bayar da tallafi na shugaban kasa da ke Abuja

- Matasan sun mamaye ofishin ne domin gudanar da tattakin nuna goyon baya ga tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Charles Dokubo

- Shugaban kungiyar ya ce sun shirya gudanar da taron wayar da kan jama'a a Abuja domin bayyana mubayi'arsu ga tazarcen Buhari a hukumance

Daruruwan matasan al'ummar Ijaw da ke zaune a jihohi 19 na Arewacin Nigeria da na birnin tarayya Abuja, suka mamaye babban ofishin shirin bayar da tallafi na shugaban kasa da ke Abuja domin gudanar da tattakin nuna goyon baya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mai taimakawa shugaban kasar ta fuskar farfado da Niger Delta, Farfesa Charles Dokubo.

Matasan da ke dauke da kwalaye masu rubutun bayyana goyon bayansu ga tazarcen shugaban kasa Buhari, sun gudanar da tattakin ne karkashin jagorancin shugaban kungiyar matasan Ijaw a Arewacin Nigeria, Comrade Akasah Eniyekeye Kelvin, wanda ya ce za su tabbata Buhari ya samu kuri'un su a zabe mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Saboda kaddamar da yakin zaben Atiku a Enugu: An garkame makarantun gwamnati

Zaben 2019: Al'ummar Ijaw sun yi tattaki a Abuja domin nuna goyon bayansu ga Buhari

Zaben 2019: Al'ummar Ijaw sun yi tattaki a Abuja domin nuna goyon bayansu ga Buhari
Source: Facebook

Akasah wanda ya ce kungiyar ta shirya gudanar da taron wayar da kan jama'a a Abuja domin bayyana mubayi'arsu ga tazarcen Buhari a hukumance, ya kara da cewa tuni shirye shirye suka yi nisa na gudanar da gangamin matasa akalla miliyan ukku na kungiyar a fadin kasar.

"Mun fito ne domin sanar da duniya ce shugaban kasa Muhamadu Buhari da Farfesa Charles Dokubo sun yi rawar gani. Tsawon watanni tara da suka gabata da shugaban kasa ya nada Farfesa Dokubo, ya yi aiki tukuru. Tun da ya shiga ofis, ya farfado da cibiyoyin horas da jama'a.

"Zamu bi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Dokubo saboda sun yi mana ayyukan da suka shafi rayuwarmu da kuma muna da yakinin cewa za su kai Niger Delta zuwa mataki na gaba," a cewar sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel