Saboda kaddamar da yakin zaben Atiku a Enugu: An garkame makarantun gwamnati

Saboda kaddamar da yakin zaben Atiku a Enugu: An garkame makarantun gwamnati

- Rahotanni sun bayyana cewa an garkame makarantun gwamnati a jihar Enugu, a yayin da Alhaji Atiku Abubakar ya dira jihar domin kaddamar da yakin zabensa

- Sai dai daliban, sun ce an umurce su da tabbata sun halarci filin wasanni na Nnamdi Azikiwe, inda Atiku ya ke kaddamar da yakin zaben na sa

- A hannu daya kuwa, wasu iyaye a jihar sun kalubalanci wannan mataki na sallamar yaransu kawai saboda wani dan takara zai kaddamar da yakin zabensa

A ranar Juma'a, an garkame makarantun gwamnati na Firame da Sakandire a jihar Enugu, a yayin da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya dira jihar domin kaddamar da yakin zabensa na ranar 16 ga watan Fabreru da ke zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ya ruwaito cewa an sallami dalibai daga makarantun gwamnati daban daban na jihar, da misalin karfe 10 na safiya, sakamakon ziyarar da Atiku ya kai jihar domin kaddamar da yakin zabensa.

Daya daga cikin daliban, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya shaidawa NAN cewa malaminsu ya sanar da shi da sauran daliban da ke a cikin jihar cewa an sallame su da wuri ne domin ziyarar da Atiku zai kawo jihar.

KARANTA WANNAN: Tsakanin Buhari da Atiku: Wole Soyinka ya fadi matsayarsa kan wanda zai zaba

Saboda kaddamar da yakin zaben Atiku a Enugu: An garkame makarantun gwamnati

Saboda kaddamar da yakin zaben Atiku a Enugu: An garkame makarantun gwamnati
Source: Facebook

Haka dai lamuran suke a kusan dukkanin makarantun gwamnatin jihar da kamfanin NAN ya kai ziyara, a garin na Enugu.

Sai dai daliban, sun ce an umurce su da tabbata sun halarci filin wasanni na Nnamdi Azikiwe, inda Atiku ya ke kaddamar da yakin zaben na sa, domin su ma su shaida.

A wani labarin kuma, wasu iyaye a cikin jihar sun kalubalanci wannan mataki da aka dauka na sallamar yaransu daga makarantar saboda kawai wani dan takara zai kaddamar da yakin zabensa.

Mr Francis Ogbu, ya ce tabbas wannan matakin da aka dauka na dakatar da koyo da koyarwa a makarantun gwamnati na jihar saboda wani mutum kawai, ya saba da dokar koyarwa ta kasa.

Ogbu ya ce bai kamata a tursasawa kananan yara shiga harkokin siyasa ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel