Tsakanin Buhari da Atiku: Wole Soyinka ya fadi matsayarsa kan wanda zai zaba

Tsakanin Buhari da Atiku: Wole Soyinka ya fadi matsayarsa kan wanda zai zaba

- Farfesa Wole Soyinka, ya ce babu wanda zai zaba tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar a zaben watan Fabreru da ke zuwa

- Soyinka ya ce a yanzu ra'ayinsa shine a samar da sabuwa gwamnati; kuma ya ce ya na da tabbacin cewa akwai masu irin wannan ra'ayin irin na sa.

- Ya ce tun tuni ne ya kamata a ce an samu wata kwakkwarar maja ta ukku, amma sai dai an samu akasi, inda kwararrun masu kwacewa, suka kwaceta tun kafin ta yi suna

Shahararren marubucin littattafan turanci a Nigeria, wanda ake yiwa lakabi da 'sahibul kalam', Farfesa Wole Soyinka, ya ce babu wanda zai zaba tsakanin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari da na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a zaben watan Fabreru da ke zuwa.

Soyinka ya bayyana matsayarsa ne a jiya Alhamis, a wani shiri mai taken: “The Civic Choice in a time of Judicial ‘Penkelemes”, wanda kungiyar al'umma (CF) ta shirya.

Ya ce: "Ni Wole Soyinka, ba zan zabi daya daga cikin wadandan manyan 'yan takarar na manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu ba, a iya nazari na, banga wani dalili da zai sa in zabe su, ina kuwa da kwararan dalilai kan hakan. A yanzu ba lokaci ba ne na tankade da rai-rai ba ne, tuni wannan ya wuce. Ni ra'ayi na shine samar da sabuwa gwamnati; kuma na tabbata akwai masu irin wannan ra'ayin nawa."

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki ga tawagar 'yan sanda, sun kashe ASP a Delta

Buhari da Atiku ba su cancanci kuri'ata ba - Wole Soyinka

Buhari da Atiku ba su cancanci kuri'ata ba - Wole Soyinka
Source: Depositphotos

Ya ce tun tuni ne ya kamata a ce an samu wata kwakkwarar maja ta ukku, amma sai dai an samu akasi, inda kwararrun masu kwacewa, suka kwaceta tun kafin ta yi suna.

A wani labarin makamancin wannan kuwa, lauya mai kare hakkin bil Adama, Femi Falana, ya ce dakatar da Alkalin Alkalai na kasa, mai shari'a Walter Onnoghen, abun a yi masa kyakkyawan hukunci ne a tsarin demokaradiyya ta kasar.

Ya kuma yi Allah-wadai da irin salon shugabancin kun giyar lauyoyi ta kasa NBA da kuma majalisar koli ta fannin shari'a NJC, bisa nuna cewa babu komai akan zarge zargen da ake yiwa tsohon CJN da aka kora.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel