Wata biyu za'a hau jirgin kasa kyauta a Najeriya, inji Osinbajo, ana gab da zabe

Wata biyu za'a hau jirgin kasa kyauta a Najeriya, inji Osinbajo, ana gab da zabe

- Osinbajo na can yana bude ssabon layin Dogo na kasar Yarabawa

- Yace kowa ya hau jirgin kyauta wata biyu

- Ansha zarginsa da kyautar da arzikin gwamnati don a zabe su

Wata biyu za'a hau jirgin kasa kyauta a Najeriya, inji Osinbajo, ana gab da zabe

Wata biyu za'a hau jirgin kasa kyauta a Najeriya, inji Osinbajo, ana gab da zabe
Source: Depositphotos

Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaba Buhari, ya kaddamar da sabbin hanyoyin jirgin kasa a yankin yammacin Najeriya a jiya, ya kuma ce zasu bari kowa ya hau danin jirgin kyauta har watanni biyu lokacin tukin gwaje-gwajen aikin.

An dai yi wannan aiki ne na layin jirgi da zai taso daga Legas ya tsaya a Badun ta jihar Oyo, birni mafi girma a duk fadin kasashen bakaken fata. Wanda zai kwashe yawancin fasinjojin dake titin mota, wanda ke yawan samun hadari.

GA WANNAN: Magun EFCC ya gargadi bankuna kan kudaden taimakawa ta'addanci dake yawo

Shi dai wannan layin dogo, ana so ne a kawo shi arewa har Kano, har ma ya wuce Arewa zuwa Daura..Amma sai an zabi shugaba Buhari za'a ci gaba, lamari da yasa ake ganin dole Yarabawa suso su zabi shugaba Buharin, wanda ya kai manyan ayyuka duk yankin nasu a zangon Farko.

Sai dai wannan kyautayi da Osinbajo yayi, na hawa jirgi kyauta har wata biyu, da ma bada bashin N10,000 ga talakawa, duk na zame wa PDP qaya a baka, inda suke zargin wadannan hanyoyi ne na sayen bakin talaka da kuri'unsu lokutan zabe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel