Ayyukan ruwa na Bukola Saraki lokacin yana gwamnan Kwara ashe wai na bogi ne - bincike

Ayyukan ruwa na Bukola Saraki lokacin yana gwamnan Kwara ashe wai na bogi ne - bincike

- Tsuguni bata kare ba; aikin ruwan Ilorin da ya lashe biliyoyin nairori duk bogi ne

- Wasu mazauna yankin sunce basa samun ruwan sai damina, wasu ma cewa sukayi babu kwata kwata

- Wasu mazaunan sun koka da cewa yayin kaddamarwa ne kawai ruwan ke zuwa

Ayyukan ruwa na Bukola Saraki lokacin yana gwamnan Kwara ashe wai na bogi ne - bincike

Ayyukan ruwa na Bukola Saraki lokacin yana gwamnan Kwara ashe wai na bogi ne - bincike
Source: UGC

Mazauna Ilorin, jihar kwara sun karyata ikirarin gwamnatin jihar na cewa ta kashe Naira biliyan 6.5 akan aikin gyaran ruwan jihar.

Mazauna Oja Oba, Maraba, Abdulazeez Attah, Jebba da kuma kewayen sun karyata aiyukan da gwamna Abdulfatah Ahmed yace yayi.

Gwamnan yace yayi aikin samar da ruwan jihar wanda ya kai har gidaje 48,000 a babban birnin jihar.

"Da kammaluwar wannan bangaren, zamu iya cewa mun aje babban tarihi na kokari wajen ganin cewa mutanen jihar kwara sun samu ruwa. Wannan aikin zai kaimu kusa da ganin cewa mu samu cimma burin mu na aiyukan cigaba na dogaro da kai na 6 wanda amfanin shi shine samar da ruwa mai kyau na sha ta kowa nan da 2030," gwamnan yace.

Amma kuma daga abinda ENetSuD, wata kungiya a kwara ta bayyana shine ba ayi wannan aikin ba a wasu wurare, inda suka gano cewa anyi a wasu bangarorin na jihar.

Kamar yanda Dr. Abdullateef Alagbonsi, mashiryin ENetSuD yace an fara aikin gyaran ruwan Ilorin ne a 2009 lokacin gwamnatin Bukola Saraki. Aikin na daya daga cikin aiyukan dake kawo cece ku ce tun a wancan lokacin. Aikin ya hadiye biliyoyin Nairori amma har yau babu amfanin su," cewar Alagbonsi.

An an kammala kashi 98 na aikin a 2014, inji mataimaki na musamman ga gwamna Abdulfatah Ahmed akan habaka hannayen jari da tsare tsare, amma shekaru bayan hakan ragowar kashi 2 da ya rage ya kasa karasawa.

GA WANNAN: Ai ko don kunyar iyali na na karasa gadar gabashin Najeriya ta 2nd Niger Bridge - Atiku

An kaddamar da aikin a 22 ga watan Nuwamba 2018.

Amma kuma mazauna jihar sai suke kokawa akan rashin ingancin aikin. Sunce lokacin kaddamarwa ne kadai yake aiki.

Wata mazauniya yankin tace lokacin damina ne kadai burtsatsen su ke aiki. Yanzu kuwa lokacin rani sai suka ji shiru kuma yanzu ne suka fi bukatar ruwan. Akwai bukatar su zo su gyara, inji matar.

Bolakale Olateju, mazaunin Oja-Oba yace shi karya ne ma ba aikin da aka yi a Oja-Oba. Yace suna fatan dai aikin ya iso yankin saboda wahalar ruwan da suke ciki.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel